Home ยป Tsagewar Dubura (Anal Fissures)

Tsagewar Mafitar Bayangida (Anal Fissures) Wani nau`in na Cuta Ne Wanda ke Sanya Tsagewa daga cikin Duburan Mutum. Wannan Cuta tana kama da Cutar Basir. Yawan Yunkuri da kuma Kumburin Ciki ke Sanya Kamuwa da Wannan Cutar a Mafiya yawan Lokuta.

Ana samun tsananin ciwo da kuma radadi a lokacin da mutum ke yunkurin yin bayangida. Sannan kuma yana Haifar da Zubar Jini daga Cikin Dubura. Ya kan Sanya Sakewar Jijiyoyin Bakin Mafitar Bayan Gidan.

Yawanci Yara Kanana suke Kamuwa da wannan cuta, Amma ta kan kama manya a wasu Lokutan.

Tsagewar Mafitar Bayangida (Anal Fissures) Cuta ce wadda bata da Wahalar Warkewa. Cin Abinci Masu Kunshe da Sinadaran Faiba, Zama Cikin Ruwan Dumi da Amfani da Man Kanunfari Kan Magance Cutar.

Alamomin wannan cuta sun hada da Ciwo mai Radadi Lokacin yin Bayangida. Ciwo Mai Radadi Bayan an yi Bayangida Wanda Kan dau Tsawon Awanni Kafin ya Lafa. Ratsin Jini Cikin Bayangida, Bayyanar Tsagewar a Mafitar Bayangida. Kumburi ko Sa’bar Fatar Bakin Mafitar Bayangida duka na cikin alamu wannan cuta.

Bayyanannun Abubuwa da kan Janyo wannan cuta sun hada da; yin Bayangida mai Tauri da Girma. Kumburin ciki da kuma yawan yunkuri yayin Bayangida da Gudawa mai Daukar Lokaci. Haka zalika, akwai Haihuwa da kuma Saduwa ta Dubura.

Cutar Kumburin Hanji, Cancer Dubura Wato Dajin Mafitar Bayangida, Cuta mai Karya Garkuwan Jiki, da Tarin TB.

Abubuwan da ke kara hadarin kamuwa da wannan cutar sun hada da Haihuwa, Kumburin Ciki, Cutar Kumburin Hanji, Saduwa ta Dubura, Karancin Shekaru Cutar Tafi yawa a yara kanana.

Tsanantar wannan cuta ta hada da wanda taki warke wa da wuri, ko ta sake dawowa bayan ta warke, da kuma tsagewar da tayi tsanani.

Za`a iya kare kai daga wannan cutar ta hanyar cin abinci masu dauke da sinadaran faiba, kare kai daga abin da kan kaifar da kumburin ciki ko gudawa. Motsa jiki yadda ya dace domin gujewa yawan yunkuri yayin bayangida.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply