Home ยป Magance Cutar Basir (Piles)

Cutar Basir (Piles) Yanayi ne da kan Sanya Kunburin Jijiyoyi daga Mafitar Bayan Gidan Mutum. Yakan zamo kamar Tsiro ta Ciki ko kuma daga Wajen Bakin Mafitar Bayan Gidan. Wannan Tsiro kan Sanya Tsananin Ciwo Da Suka Hada Da Zugi, a Wani Lokacin Yakan Hana Mutum Zama.

Alamomin Cutar Basir na da alaka da yanayin kumburin, ta ciki ne ko waje. Ga mai Basir ta ciki, Alamomin sun hada da yawan Yunkurawa da kuma Kaikayi Yayin Bahaya. Sannan Kuma ya kan Sanya Tsagewar Mafitar Bahaya da kuma Jini Cikin sa. Kumburin ko tsiron da ya fito waje kan sa tsananin zugi, ciwo dama Kaikayi.

Lokacin da kumburin ya kasance daga wajen mafitar bayan gidan, ya kan sa kaikayi a duburan baki daya. Tsananin zafi da rashin kwanciyar hankali, kumburi da ma zubar jini. Taruwar jini cikin wannan kumburin kan daskare ya zauna a matsayin tsiro mai tauri da kuma ciwo. Wannan kan tsananta ya haifar da wata cutar daban.

Ana kamuwa da cutar Basir ta hanyar yawan yunkuri wajen yin bahaya. Yawan zama musamman a kan bayan gida, lokacin da mutum ke gudawa ko kumburin ciki da mummunan kiba ko teba.

Yawan cin Abinci Mai Tauri, Ko Yawan daga Abu Mai Nauyi ko Saduwa ta Dubura ga wasu Mutanen Yakan haifar musu da Cutar Basir (Piles).

Sakewar Jiki Saboda Tsufa ko yawan Shekaru na kara hadarin kamuwa da wannan cutar. Haka zalika Wani sa`in Mata Masu Juna Biyu na kamuwa da wannan ciwo saboda yanayin canjin jiki da kuma nauyin abin da ke cikin su.

Masu fama da Wasu Cututtukan da suka hada da Gudawa ko Kumburin ciki, Rashin Samun Abinci Dake da Wadataccen Sinadarai Irin Su ‘Ya ‘ Yan Itace Da Kuma Nauin Kayan Ganye Kamar Su Faiba, Vitamins, suma na cikin hadarin kamuwa da Cutar Basir. Yanayin Sana`a ko dabi`ar mutum da ta kunshi yawan zama kan zamo hanyar kamuwa da cutar.

Hanya mafi sauki da inganci wajen kare kai daga kamuwa da cutar Basir shine cin abinci ko abun sha da zai hana bahaya yin tauri.

Wadannan shawarwari kan taimaka wajen kare kai daga Basir. Na farko shine yawan cin abinci masu dauke da sinadarin Faiba kamar ganyayyaki da yayan itatuwa. Anfani da dangin hatsi wanda aka sarrafa ba tare an surfa su ba na wadata jiki da sinadarin na faiba.

Na biyu, Yawaita shan ruwa. Shan akalla kofi shida zuwa takwas na ruwa a kowace Rana tare da wasu nau`i na abin sha zai taimaka. A kiyaye shan giya Barasa kuma.

A Guji yawan yunkurawa a lokacin da ake bahaya. Yunkurin kan Sanya jijiyoyin kumbura su haifar da wannan cuta.

Motsa jiki wata hanya ce da mutum zai rage kiba. Kiba na cikin abubuwan da ke haifar da wannan cuta. Lazimtar motsa jiki da kuma bin hanyoyin rage kiba na da anfani.

Daga Karshe a Kiyayi yawan zama, a lokacin da aikin mutum ya hada da yawan zama, a dan samu a matsa kafafuwa kadan bayan dan lokaci. Sannan idan da hali a zauna kan abu mai laushi.

Tsanantar Cutar Basir (Piles) na da hadari ga lafiyar jikin dan adam baki daya. Ta kan hana ayi aiyukan yau da kullum da kuma haifar da wasu Munanan Cututtuka a cikin jiki.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos