Home » Ciwon Damuwa (Depression)

Ciwon Damuwa Wato (Depression) Wani Yanayi Ne da Mutum ke shiga wanda ke Sanya yawan fushi da kuma rashin son Shiga Jama’a. Yanayin Yana Shafar Yadda Mutum Yake Ji, Tunani da kuma Mu`amala. Yakan Janyo Matsalolin Kwakwalwa, Lafiyar Jiki. Cutar Tana Shafar al`muran Mutum Na Yau da Kullum. Har Ta Kai Ga Mutum Ya Dinga Jin Gara ya Mutu.

Kamuwa da Ciwon Damuwa ba Kasawa Bace, Sannan Kuma ba`a iya fita Daga cikin ta a lokaci guda. Tana bukatar Matakai da dama na Warkewa.

Wannan Cuta na Kama Mutum Sau Daya a Rayuwa amma kuma takan taso sau Dayawa Kafin ta Warke. Alamomin ta sun hada da;

 • Yawan Fushi, Son yin Kuka, Jin Rashin Amfani ko Rashin fa`idar Rayuwa.
 • Yawan Masifa, Bacin Rai kan abin da bai kai ba.
 • Rashin son yin abubuwan da mutane ke samun nishadi cikinsa Kamar Jima`i, Wake-Wake, Kallo da Sauransu.
 • Matsalar Bacci Kamar Rashin Bacci ko Yawan Bacci
 • Yawan gajiya da rashin kuzari
 • Rashin son cin abinci, Rama, yawan cin abinci da Karin kiba
 • Tsoro da Tashin Hankali
 • Tunani, Magana da motsi cikin Rashin Kwarin Jiki
 • Tuhumar kai kan abin da ya wuce, jin rashin fa`idar rayuwa.
 • Rashin mai da hankali, yanke shawara, da tuna abubuwa.
 • Tunanin Mutuwa, tunanin kashe kai da yunkurin kashe kai
 • Ciwon kai da ciwon jiki.

Yawancin mutane dake fama da ciwon Damuwa, alamomin suna bayyana sosai yadda matsalolin su zasu shafi aikinsu na yau da kullum.

Yara na nuna alamun damuwa kamar na manya sai dai sukan nuna alamu da yawan kuka, rashin son zuwa makaranta da kuma rama. Rashin kokari a makarantar.

Ga wadanda suka manyan ta, Ciwon damuwa baya daga cikin alamomin tsufa. Amma yawanci ana gani kamar ba matsala bace kuma ba`a neman magani. Sukan yi fama da Mantuwa, Canjin yanayi, Ciwon Jiki, Gajiya, Rashin Son cin Abinci, Gudun Jima`i da son Kebanta kai.

A lokacin da mutum ya fuskanci wani nasa na cikin wannan yanani, yana da kyau a tuntubi likita, kuma a kasance kusa da su a Kowane Lokaci.

Abubuwan da ke haifar da wannan ciwo ba a bayyane suke ba, sai dai akwai wadanda ake alakan ta su da ciwon kamar Samun canji na yanayin kwayoyin halitta, Matsalar kwakwalwa da Gado.

Wasu daga cikin abubuwa dake kara hadarin kamuwa da ciwon sun hada da.

 • Mata sun fi kamuwa da wannan ciwon fiye da maza sai dai mata na neman taimako
 • Asalin masu rashin kwarin Guiwar yin abu
 • Wani al`amari da ya faru da ya tada hankali kamar cin zarafi na Zahiri, Fyade, Mutuwar Makusanci, Yaudara ko Matsala ta Dukiya.
 • Ciwon Cikin Dangi na kusa
 • Kasancewa Mai Luwadi ko Madigo, Mata-Maza, Dan Daudu ko Wadanda Halittarsu ta Jinsi Bata Cika ba.
 • Shaye-shaye
 • Cutar Daji, Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki (HIV), Shanyewar Barin Jiki ko Ciwon Zuciya.
 • Wasu Magungunan Asibiti na Cututtuka Kamar Hawan Jini, Maganin Bacci da Sauransu.

Ciwon Damuwa (Depression) na tsananta idan ba`a magance shi ba. Babu wani takamanman hanyar kariya daga wannan ciwo. Sai dai masana sun ba da  wadannan shawarwari da zai taimaka.

 • Rage Gajiya
 • Tuntubar iyalai da dangi lokacin Damuwa
 • Neman magani da Zarar wasu alamu sun nuna
 • Kasancewa kan magani na tsawon lokaci domin gujewa dawowar ciwon

Ayi kokarin kare kai daga shiga damuwa domin ingantacciyar lafiyar kwakwalwa da rayuwa mai inganci.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos