Home » Motsa Jiki

Motsa Jiki yana da amfani matuka ga rayuwar Dan Adam. Abu ne wanda ya kamata ace anayin sa a ko da yaushe.  Dukkan sassan jikin Dan Adam na anfana a yayin da mutum ke motsa jikin.

Aikin motsa jikin na sa mutum cikin farin ciki da kuzari, yana taimakawa lafiyar jiki da lafiyar zuciya baki daya.

Haka zalika, motsa jiki na kare mutum daga kamuwa da larura da cututtuka daban daban kamar ciwon suga, mummunan kiba ko teba, amosanin guyiwa da sauransu.

A ko wani lokaci motsa jikin na bukatar tsari da kuma Iyawa. Bukatar sanin adadin abin da mutum zaiyi da kuma lokaci da ya kamata ayi shi na da anfani.

Har wa yau akwai bukatar tantance lafiyar mutum domin sanin irin motsa jikin da ya dace da shi.

Ana bukatar mutum ya sani cewar motsa jiki na bukatar binciken masana. Domin su daura mutum kan tsarin da ya dace da shi. Hakan zai taimaka wajen rashin tsananta wasu matsaloli ko cututtuka da mutum ke da su.

Matakai guda uku ake bi a lokacin da mutum zai fara motsa jikin. Na farko shine  binciken masana don tabbatar da lafiya da kuma nauin motsa jiki da mutum ke bukata.

Na biyu kuma, soma wa da kadan-kadan wanda zai bawa jikin daman shiryawa dangane da aikin da za`a gudanar.

A karshe akwai aikin kacokan. Shi kuma yana nufin  lokacin da mutum zai motsa jikin sa yadda ya dace da bukatar jikin. Sa`annan a samu biyan bukata.

Rashin bin wadannan matakai kan zama barazana ka jikin mutum hada da lafiyar sa.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos