Cholera Cuta ce Ta Gudawa Dake Kama Mutane ta dalilin Kwayar Cutar bacteria vibrio.
Akalla Kimanin Mutane Miliyan Hudu 4,000,000 Ne Ke Kamuwa da Cutar duk Shekara a Fadin Duniya Yayin da Kimanin Mutum Dubu Dari da Hamsin 150,000 Ke Mutuwa Sakamakon Cutar a Fadin Duniya.
Ana Samun Cutar Cholera Ne a Cikin Ruwa Ko Abinci da ya gurbata da Kwayoyin Cutar. Ana Samun Cutar Ne a wurare Marasa tsafta, Gurbataccen Ruwan Sha da Sauransu.
Alamomin Cutar sun Hada da Yawan Gudawa, Amai, Rashin Kwarin Kafafuwa Da Rashin Ruwa a Jiki. Alamomin Suna Fara Bayyana awa Biyar Bayan Shigar Cutar Jikin Mutum.
Ana Shawartar Mutane da Zarar sunga Wadannan Alamomi to su garzaya Zuwa Asibiti Mafi Kusa Kuma a Dinga Amfani da Ruwan Gishiri da Suga Wato ORS.
Add comment