Home » CUTA MAI KARYA GARKUWAR JIKI (HIV)

Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki Wato (HIV). Cuta ce dake lalata Garkuwar Jikin Dan Adam ta Sanya ya kasance baya iya yakar cututtuka idan suka zo shiga jiki.

Wannan Cuta ta kan Tsananta idan ta Dau Tsawon shekaru ba`a mata magani ba, Sai zamo Kanjamau wato (AIDS). A halin yanzu, bincike ya bayyana cewar yawancin mutane da ke da wannan cuta ta HIV na karban magani. Hakan ya Sanya ba`a cika samun masu cutar ta Kanjamau ba.

Ana kamuwa da wannan cuta mai karya garkuwan jiki ta hanyar haduwar jini, saduwar aure, ko daga uwa zuwa `da a lokacin haihuwa ko shayarwa.

Har wa yau, likitoci basu gano magani na wannan cuta ba. Sai dai, akan bada magunguna da zasu kawar da alamomin cutar da kuma hana cutar tsanan ta.

Alamomin cutar HIV ya banbanta bisa ga tsanantar cutar a cikin jiki. Wasu mutane kan nuna alamun Mura cikin sati biyu zuwa hudu da kamuwa. Amman wannan zai kauce daga baya. Wasu kuma basu nuna alamu Kwata-Kwata a wannan lokaci.

Yawancin mutane kan nuna wadannan alamomi a lokacin da cutar ta bayyana a jikin su. Zazzabi, Ciwon Kai, Ciwon Jiki da Gabobi, Fesowar Kuraje, Ciwon Makogoro da Kurajen Baki. Sannan akwai Kumburin Gabobi, Kafa, da Wuya, Gudawa, Rama, Tari, Yawan Zufa musamman cikin dare da sauransu.

Wadannan alamomin basu cika bayyana sosai na ta da hankali a wannan lokaci ba. Sai dai yana da matukar hadari da kuma saurin yaduwa a lokacin. Farkon lokacin da mutum ya kamu da wannan cuta ba ta nuna alama sannan kuma bata bayyana ko da a cikin gwaji ne. Sai bayan wasu lokuta Sannan gwaji yake bayyana Cutar.

Rashin Shan magani na wannan cuta kan haifar da cutar Kanjamau wanda ke nuna cewar dukkan garkuwar jikin dan adam ta lalace. Hakan zai haifar da kamuwa da sauran munanan cututtuka a jikin mutum kamar Daji Wato Cancer.

Cuta mai karya Garkuwar Jiki (HIV) dai cuta ce da kwayoyin cuta na Bairos ke kawo ta. 

Ana kamuwa da cutar idan saduwar aure ta faru da mai dauke da wannan cuta. Na biyu akwai anfani da abubuwa masu kaifi tare da mai dauke da cutar. Ko lokacin da aka kara jinin mai dauke da cutar ga wanda ba shi da shi. Ga mace Mai Juna Biyu da ke da cutar HIV, `dan da ta Haifa kan iya kamuwa da cutar a ciki, lokacin haihuwa, ko shayarwa.

Ba`a daukar wannan cuta ta hanyar mu`amala ta yau da kullum da mai dauke da cutar. Runguma, Sumbata, hada hannu, taba jiki. Ba`a Shakar ta a iska ko shan ta a ruwa. Haka zalika cizon kwari baya kawo wannan cuta.

Wannan cuta bata ware shekaru, jinsi, launin fata ko makamantan su. Amma akwai wasu abubuwa da kan kara hadarin kamuwa da cutar.

Mu`amalar aure barkatai ba tare da kariya ba na daga cikin abin da ke kara hadarin kamuwa da cuta Mai karya garkuwan jiki. Ga masu maye ta hanyar saka allura. Su kan yi anfani da allura guda daya su dayawa. Kuma a lokacin da akayi rashin dace dayan su na dauke da wannan cuta, dukkannin su zasu kamu da ita.

Yawancin masu cutar HIV na cikin hadarin kamuwa da cututtuka kamar Tarin TB, Wanda aka fi Sani da Tarin Fuka, Sanyin Mara, Daji, Ciwon Ido, Kunne, Huhu, Ciwon Hanta, Koda, Zuciya da Matsalar Kwakwalwa.

Hanyoyin kariya daga wannan cuta sun hada da;

  • Shan Magani ko Allura wanda ake kira da PrEP a turance. Wannan zai taimaka wajen kare kamuwa da cutar da kaso mafi girma da wanda ya sadu da mai cutar.
  • Daukan Magani ga mai dauke da cutar. A yayin da mai dauke da wannan cuta ke karban magani yadda ya dace, zai taimaka wajen kare dayan su wanda ba shi da cutar. Wannan shi ake kira TasP. A wannan tsari dole ne ya kasance ana shan magungunan bisa tsari a dai-dai lokaci da aka gindaya.
  • Shan Magani bayan zaton anyi mu`amala da mai cutar. Shan wannan magani cikin awanni saba`in da biyu wato kwanaki uku da yin mu`amalan zai taimaka wajen rage hadarin kamuwa da cutar.
  • Yin anfani da kororon roba a lokacin saduwar aure da mai dauke da cutar. Tabbatar da cewa sabo ne domin gudun anfani da wanda ya riga ya fashe.
  • Sanar da dayan yayin mu`amala dangane da cutar da ake da shi.
  • Idan bukatar yin allura ta taso, yin anfani da sabo a ko wani lokaci.
  • Anfani da shawarwarin likita ga mai juna biyu da ke da cutar dangane da cikin, haihuwa da kuma shayarwa.
  • Yin kaciya ga `da namiji na rage hadarin kamuwa da cutar mai karya garkuwan jiki

Yawancin cututtuka na da alamomi masu kamanceceniya. Don haka, yana da matukar muhimmanci a tuntubi likita a duk lokacin da mutum ya fuskanci canji a cikin jikn sa.

Mai Dauke da wannan cuta na iya rayuwa mai inganci kamar kowa a lokacin da yake karban magungunan cutar kuma yake anfani da Su ta Hanyar da ya dace.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos