Home » KARANCIN JINI A JIKI (ANEMIA)

Karancin Jini a Jikin Mutum na faruwa ne a lokacin da kwayoyin jinin jiki da ke yada sinadarin Oksijin sukayi karanci a cikin jini. Dalilai da dama na Sanya faruwan hakan. Kuma wannan na jawo matsaloli da dama ga jiki.

Karancin Jinin kan iya kasancewa na lokaci kadan ko kuma tsawon lokaci. Haka zalika ta kan zamo sama-sama ko kuma ta tsananta. Amma yawanci, idan aka samu karancin jini a jiki (Anemia) ta kan nuna alama ne na wata cuta da ke Shirin kama mutum ko kuma ta riga ta kama mutum.

Akan iya magance wannan yanayi ta Hanyar shan magunguna, Karin jini ko cin nau`ukan abinci da ka iya wadata jikin dan adam da jinin da yake bukata.

Lokacin da jini yayi karanci a jikin mutum, yakan nuna alamu da dama. Wani lokaci ba`a ganewa sosai idan ba ta sananta ba. Wadannan alamomin sun hada da Yawan Gajiya da Kasala, Nunfashi Sama – Sama da Karin Bugun Zuciya. Jiri, Rashin Karfin Jiki, Ciwon Kirji, Ciwon Kai, Rashin Karfin a Hannaye da Kafafuwa. Yin fari na fata wanda akasari anfi samun wannan a fararen fata.

Mutum kan shiga wannan yanayi ne a lokacin da kwayoyin jini da ake kira Hemogulobin a turance sukayi karanci a jiki. Abubuwan da ke janyo karancin sun hada da rashin samar da kwayoyin da jiki ke yi. Yawan zubar da jini akai-akai wanda ba zai bada damar jiki ta samar da madadin su ba. Abu na karshe akwai lalata kwayoyin jinin da jikin kansa ke yi a wani yanayi.

Karancin sinadarin Ayon (Iron) a jiki na Sanya jini yayi kadan a jiki. Saboda Bargon jikin mutum na bukatar wannan sinadari domin samar da jini. Karancin sinadarin na Sanya rashin gudanar da aiki ga bargon sai kuma jinin yayi kadan a jiki.

Mata masu Juna Biyu na shiga wannan yanayi idan ba su shan magungunan da zai kara musu sinadarin Ayon. Akan iya Zubar da Jini a Lokacin Al`ada, Jin Ciwo Mai Tsanani, Ciwon Daji da Sauransu.

Haka zalika, Karancin Sinadarin Bitamin a jiki na Sanya rashin samun ishashshen jini.

Wasu Cututtuka Kamar Daji, Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki (Sida), Ciwon Koda da Amasanin Gaba na Sanadin Rashin Samun Wadataccen jini a jiki.

Mu`amala da wasu Kemicals daga masana`antu na Sanya Jiki samun Lahani da zai hana shi samar da sabon Kwayoyin Jini.

Cututtuka kamar su Dajin Jini da Amosanin Jini na Sanya mutuwar Kwayoyin Jini cikin Kakanni lokaci. Kuma bata ba da damar jiki ta maye gurbin su cikin lokaci da ya kamata.

Abubuwan da ke kara hadarin samun Karancin Jini a jiki sun hada da cin Abincin da bashi da Muhimman Sinadarai. Matsala a Karamin Hanji da kan hana ta tatsar sinadarai masu anfani a cikin abinci, yawan zubar jini lokacin al`ada. Masu Juna Biyu da ba su shan Magungunan Awo da wanda ke da wasu cuttukan kamar Dajin Jini, Amosanin Jini, Ciwon Suga da Sauransu.

Tarihin wannan yanayi cikin dangi, Shan Giya, Shekaru Girma, zama a wasu masana`antu masu anfani da Kemikals, su ma da daga cikin abubuwan da ke kara hadarin shiga wannan yanayi.

Idan ba`a Magance shi ba, Karancin Jini Kan Sanya a samu tsananin gajiya da kasala da kan hana mutum yin komai na rayuwa. Ga masu juna biyu, ta kan sa bari ko haihuwa kafin lokaci, ga dan da bashi da ishashshen lafiya. Ta kan haifar da Kumburin Zuciya, Bugun Zuciya da kuma wasu Matsalolin Zuciya baki daya.

Idan yayi tsanani, ya kan kashe mutum lokaci guda.

A yawancin lokuta, karancin jini a jiki abu ne da ba za`a iya kare faruwan shi ba. Sai dai cin Abinci mai Inganci, masu dauke da Sinadarai masu anfani na kare yawancin nau`in karancin jinin jiki. Shan magungunan Awo ga mai juna biyu, da kuma kula da lafiya ga masu fama da wasu cututtukan daban zai taimaka matuka wajen wadata jiki da adadin jinin da ake bukata domin rayuwa tayi kyau.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos