Home ยป Lafiyar Zuciya

Lafiyar zuciya na da alaka sosai da sauran sassan jikin mu kamar su kwakwalwa, koda, huhu, mahaifa da dai sauransu.

Canjin yanayin abincin da muke ci na da tasiri sosai wajen inganta lafiyar Zuciyar mu.

Amma wannan na daga cikin abubuwan da ke janyo matsalolin zuciya cikin al`umma musamman a kasar Najeriya.

Rayuwar jin dadi a lakacin Yaranta, kan janyo illoli game da lafiyar zuciya a lokacin tsufa.

Wannan illolin sun hada da ciwon zuciya, shanyewar barin jiki, cututtukan hanyoyin jinni, cutar mantuwa, rashin karfin mazakuta da sauransu.

Wadannan abubuwa na Sanya tsoro cikin zukatan al`umma amma bukatar itace canza yanayin rayuwa zuwa lafiyayya don inganta gaba.

Binciken masana ya bayyana cewar shan suga mai yawa da yawan cin naman da aka Sanya sinadarai don kare shi daga lalacewa na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da cutukan zuciya.

Wasu likitocin sun bayyana cewa cin abinci a lokacin da mutum kejin yinwa kadai na daya daga hanhoyin kiyaye lafiyar zuciya.M

Ana Shawartar Mutane Su Musanya cin abubuwa masu maiko da aka sarrafa su kamar su ayiskrim, nama, alawa, bota da sauransu Zaa Iya Maye Gurbin Su Da Man Zaitun, Abokado, dangin Gyada da sauransu a samu biyan bukata.

A madadin cin abinci a kwanta, samu lokutan motsa jiki a kullum a huta a lokacin da aka ji gajiya.

A sauya nama da kaza da su wake don samun sinadarin frotin da ake bukata.

Alawa and sauran kayan makulashe a sauya da yayan itatuwa don inganta lafiyar zuciya.

A madadin yawan surutu a kwanta ayi bacci zai fi amfani ga lafiyar zuciyan Dan Adam dama sauran sassan jikin dan adam.

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos