Home ยป Tarin TB wato Tuberculosis

Tarin TB wato Tuberculosis wani cuta ne na tari wanda kwayoyin cutar Barteriya ke kawo shi.

Wannan cuta ta Tarin TB na shafan huhun Dan Adam ne sannan ya yadu sauran gabbai masu alaka da nunfashi.

Ana iya daukara Tarin TB a yayin da mai dauke da ita yayi tari, atishawa, Dariya, ko Magana da karfi.

Kwayoyin Bakteriyan mai cutar na iya tashi ya koma kan na kusa da shi yayin da ya yi wannan abubuwa.

Haka zalika wannan cuta ta TB na saurin yaduwa a wajajen da ke da cunkuson mutane.

Masu raunin garkuwar jiki sun fi saurin kamuwa da wannan cuta ta TB musamman ma masu cutar HIV.

Yawan zama waje guda da mai wannan cutar inda babu gudanar iska sosai na daga cikin hadarin kamuwa da ita.

Alamomin wannan cutar sun kasu kashi uku.

A Matakin farko wannan cutar bata da alama sosai sai dai kamar na jin gajiya, yanayin zazzabi ko tari sama-sama.

A mataki na biyu, Cutar Tarin TB bata bayyana alamomi sosai saboda Garkuwar jiki na samar da kariya daga gareta.

Matakin karshe lokacin da cutar ta yi tsanani a cikin huhun Dan Adam takan bayyana alamomi da dama.

Wadannan alamomi sun hada da tsananin tari, tarin jinni, ciwon kirji yayin nunfashi ko tari, Zazzabi, yawan gumi da daddare.

Sannan akwai Rama, Rashin cin abinci, Gajiya, Jin sanyi ko zafi a wani bangare na jiki da cutar ta shafa.

Cutar Tarin TB na iya shafan sauran bangarorin jikin Dan Adam kamar su Koda, Hanta, jijiyoyi. Kashi da al`aura.

A yara kanana tana Sanya su yawan Amai, Rashin cin abinci, Yawan kuka da dai sauran su.

Alamomin cutar na kama da cututtuka da dama. Yana da kyau a tutubi likita a duk lokacin da aka fahimci canjin yanayi.

Akwai abubuwa da ke ingiza hadarin kamuwa da cutar Tarin TB duk da cewar kowa zai iya kamuwa da ita.

Zama damai dauke da cutar a wurin da ke da cunkuso sosai da kuma shiga garin da cutar ta barke.

Cututtuka kamar HIV, Suga, Ciwon koda, Jeji, Cutar yinwa na kara hadarin kamuwa da cutar Tarin TB.

Masu shaya-shayen giya ko taba, da masu shan magunguna barkatai suma na cikin hadarin kamuwa da cutar.

Idan likitoci suka tabbatar ka na dauke ta Cutar tarin TB, a satuka 2 zuwa uku na farko ka kare wasu daga kamuwa da Cutar.

Karban magani, kaben ta kanka, zama inda ke da gudanar iska, da sanya takunkumi yayin muamala da wasu na wasu daga cikin hanyoyin kare wasu daga kamuwa da wannan cutar.

A wasu kasashen ana iya samun allurar riga kafin wannan cuta ta Tarin TB.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos