Home » CUTAR KUMBURIN HANJI (Crohn’s Disease)

Kumburin Hanji (Crohn’s Disease) kamar yadda sunan yake, Cuta ce da ke sa Kumburi Cikin Hanyoyin Abinci na Jikin Mutum. Wannan cuta na shafar dukkan hanyoyin da abinci ke bi cikin jiki har zuwa Mafitar Bayangida. Sai dai Cutar Tafi Shafar Karamin Hanjin Mutum.

Wannan cuta na da Matukar Hadari, ta kan Sanya Tsananin Ciwo, Damuwa da Kuma Janyo Manyan Matsaloli a lokacin da ta Tsananta.

Alamomin Cutar Kumburin Hanji sun hada da, Gudawa, Zazzabi, Gajiya, Ciwon Mara, Jini Cikin Bahaya, Kuraje Cikin Baki da Rama. Rashin son cin Abinci, Ciwo da Zugi a Mafitar Bayangida.

A lokacin da wannan Cuta tayi tsanani, ta kan shafi wasu sassan jiki daban kamar; Ciwon Ido, Gabobi da kuma Fatar Jiki. Kumburin Hanta da Madaciya, Ciwon Koda, Karancin Jini a jiki, Rashin Girma da Kuma Rashin Balaga ga Yara.

Har a yanzu, Likitoci basu Gano asalin Abubuwan da ke Janyo wannan Cuta ta kumburin Hanji ba. Amma akwai wasu abubuwa da kan hassala wannan cuta. Wadannan sun hada da; Kwayoyin Garkuwan Jiki, a lokacin da jiki ke Shirin yakar wata cuta da take Shirin shiga, wannan cuta kan hassala a cikin jiki. Abu na biyu shine ana Iya gadon cutar.

Wasu daga cikin ababen da ke kara hadarin kamuwa da wannan cuta sun hada da; Shekaru, Tarihin Cutar a Dangi, Al`adu, Shan Taba, Shan Wasu Magunguna Kamar Ibuprofen da Makamantan su.

Lokacin da wannan cuta ta tsananta, ta kan haifar da rashin samun Bayangida. Wanda kumburin hanjin ke Sanya ya toshe kuma ya hana gudanar abinci a cikin sa.

Ta kan Haifar da Kuraje Cikin Hanji, Baki, Mafitar Bayangida har ma da Al`Aurar Mutum. Abu na gaba shine Tsagewar Hanjin ta hade da wata gaba daban a cikin ciki. Basir na daya daga Cikin Cutukan da kumburin hanjin ke Janyowa.

Cutar Yunwa, Cutar Fatar Jiki, Karancin Jini a Jiki, Cutukan Daji na Sassan Jiki Daban-Daban da Daskarewar Jinin Jiki.

Wannan cuta ta Kumburin Hanji bata da takamanman magani. Sai dai likitoci kan bada magungunan kawar da alamomin cutar a jikin dan adam. Wannan zai bada damar masu cutar su sami sauki cikin abin da ke damun su.

 

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos