Home » Kanunfari (Cloves)

Kanunfari (Cloves) Magani ne Sadidan Tun Zamanin Kaka da Kakanni. Ana Amfani da Man shi, Ganyenshi, Sassakenshi da kuma YaYan. Kanunfari. Magani ne na Matsalolin da suka a Shafi Ciki, Baki, Gashi, Fata da Sauransu.

An  san Wannan Itaciya Kanunfari (Cloves) da Rage Radadin Ciwo ko Wanne Irine.

Ana Amfani da Man Kanunfari Wajen Magance Matsalolin Ciki da Suka Hada da Kumburin Ciki, Gudawa, Kabar Ciki, Tari, Tashin Zuciya da Amai.

Ga abin da ya shafi Baki, ana Amfani da shi wajen Magance Warin Baki. Ana Sanya shi a Kan Hakori Mai Ciwo Don Rage Radadin Ciwon da Sauran Yanayi na Ciwo ko Tsutsar Hakori. Haka Zalika Yana Maganin Ciwon Wuya, Kuraje ko Ciwon Makogoro.

Cikin Hadin Wasu Sinadarai, ana Amfani da shi Wajen Magance Saurin Inzali ga Maza. Bincike ya Nuna Cewar Man Kanunfari da Girfa Tare da Wasu Sinadarai na Taimakawa Maza Idan Suka Shafa shi don Magance Saurin Inzali.

A Cikin Abinci, ana Amfani da Kanunfari a Matsayin Kayan Kanshi. Sannan yana Kara Dandano ga wasu Ababen sha.

Saboda Tarin Amfani da wannan itaciya ke dashi, ana Sanya shi cikin Sarrafa Sabulu, Man Goge Baki, Turare, Kayan Kwalliya kai Harma da Sigari Domin Rage Karfin ta da Warin ta.

Tsagewar Dubura Wato Mafitar Bayangida; ana Shafa Man Kanunfari na Tsawon Makonni 6 don Kawar da Wannan Cuta. Bincike ya Nuna Cewar wannan yafi Dukkan Wani Maganin sanya Laushin Bayangida.

Tsutsar Hakori; ana Amfani da Man Goge Baki Mai Dauke da wannan itaciya da kuma wasu Sinadaran na Warkar da Ciwon Hakori da ma Zubar Jini na Dadashi. Ga wanda aka Cirewa Hakori Bisa Wani Dalilin, anfani da Kanunfari a Wajen Kan Taimaka Wajen ya Warke da Wuri. Sannan kuma zai Hana Bushewar Wajen yadda ba`a so.

Ana anfani da shi wajen Kawar da Sauro da Kwari daga Cizon Mutum. Shafa man Kanunfari a Jiki na Kawar da su na Tsawon Awanni 5 bisa ga binciken da aka gudanar.

Rage Ciwo; shafa man Kanunfari Mintuna 5 Kafin ayi Allura ga mutum kan Sanya Rashin Jin Zafin Allurar.

Ga Yawancin Mutane, anfani da wannan itaciya bata da wani illa. Sai dai yawan Sanya shi a Baki da Yawa kan Jawo Ciwon Dadashi.  Amma har yanzu ba`a gano ko shan shi da yawa kan Cutar da Mutum ba.

Shan Tabar da ke Kunshe da Kanunfari na da illa ga Huhu. Kamar yadda Sauran Taba Sigari ke da shi shima yanada illa ga sauran sassan jiki.

Saboda Karfin Kanunfari, Tauna shi a Baki na Kashe Wasu daga Cikin Muhimman Kwayoyin Halittar Baki.

Ga Yara Kanana; Bai inganta a Basu Mai ko Garin Kanunfari ba. Wannan zai iya Janyo musu Cutar Hanta, Suma, da Sauran Cututtuka.

Mata Masu Juna Biyu da kuma Masu Shayarwa na iya Amfani da shi. Ba shi da wata illa a garesu. Amma a Guji Shan shi Dayawa.

Kanunfari (Cloves) na Dauke da Sinadarin da ke Rage Daskarewar Jini a Jiki. Saboda wannan, yana da Muhimmanci ga Masu Fama da Wani Yanayi na Zubar Jini su Kaucewa Shan Shi. Haka zalika, ga wanda za`a yi wa Aiki a Asibiti. Yana da Muhimmanci su Daina Shan shi Sati Biyu Kafin Aikin. A Lokacin da Mutum ke kan wani Magani mai Hanawa ko Rage Daskarewar Jini, Yana da Kyau ya Dakatar da shan Kanunfari Don Gudun fin Abunda ake Bukata.

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply