Home » Tsutsar Hakori

Ciwan Hakori ko tsutsar hakori kanyi sanadi cututtuka da dama a jikin dan adam,wanda wani lokaci kan kai ga rasa rai.

Cin  Hakori ko tsutsar Hakori wanda likotoci suka bayyana cewa babu wata tsutsa a hakorin mutum  da zata iya haddasa masa wannan rarakewar hakorin face ragowar abinci da akaci ya kan iya  haduwa da kwayoyin halittar bakin su shiga cikin hakorin har ta kai ga sun bula hakorin sannan kuma su tafi zuwa jijiya su yi mata illa.

Wannan ciwan hakorin kanyi sanadin  cututtuka da dama Kamar ciwon Huhu, ciwon zuciya,ciwon Noma, cutarDaji, da ma haifarwa mai juna biyu cutar da zata shafi dan tayin dake cikin ta, ta yadda zata haifi da marar nauyin daya dace,ko yazo da cutar nan da ake kira Noma, inda ake haifan yaro ba wani bangare na naman baki ko hanci,Duk ta sanadin ciwan Hakori da mai juna biyu ke da shi wanda zai iya haifar mata da matsalar.

Wannan ya fito ne cikin tattaunawar da muka yi da likitan hakori Dr Nura Ali Sa’id Shugaban Likitocin Hakori Matakin farko, Inda yayi kira ga Al’uma da su dinga zuwa wajan likita da zarar sunji hokorin su na ciyo. Ya kuma shawarci aalumma da su kula da lafiyar baki da hakoran su don kaucewa wannan ciwo,tare Da kokarin wankin hakori a asibiti akalla sau biyu shekara.

Haka kuma Gwamnatin Kano ta Kara Samar da Cibiyoyin kula da hakori a matakin lafiya na farko har sama da guda talatin a fadin jihar Kano da Samar da kayan wankin hakora don kaucewa matsalolin hakori.

Suwaiba Abdullahi Sarki

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos