Home » Renon Ciki

Abincin Mace Mai Juna Biyu, Me Yakamata Mai Juna Biyu ta ci? Ingantaccen Abinci Mai Gina Jiki Wanda Zai Inganta Lafiyar Mace Mai Juna Biyu da kuma Abunda ke Cikin ta. Sanin Abincin da zai taimaka ga lafiyar su na da Matukar Muhimmanci.

Lokacin da mace ke da juna biyu, ana Bukatar yin Amfanin da abin da zai inganta mata lafiya kamar yadda yake da muhimmanci ga kowa.

`Ya`Yan Itatuwa Ko Kayan Marmari, Ganyayyaki, Hatsi, Lafiyayyen Kitse da Kuma Sinadarin Frotin sune Manyan Abubuwan Da ake Bukata.

Likitoci Da Masana abinci sun bayyana wasu daga cikin abubuwan da ke da muhimmanci ga masu Juna Biyu da kuma abin da ke cikin su.

Na farko Sinadarin Folet da Folic asit; wadannan sinadaran suna taimakawa Kaifin Kwakwalwa da kuma Kare Matsalolin Kashin Baya a Kullum. Folet dai Yana Dauke da Sinadarin Vitamin B, kuma ana samun Shi ne a cikin magungunan da ake bawa mace Lokacin awo. Sannan kuma ana iya samun sa Cikin Koren Ganye Kamar Alaihu, Wake, Da `Ya`Yan Itatuwa Masu Dan Tsami Kamar Lemu.

Yana da Muhimmanci Mace Mai Juna Biyu ta Kula da Shan Magungunan da ake bata a Lokacin awo domin samun wadatar wadannan Sinadarai.

Na Biyu Sinadarin Kalshiyom; wannan sinadari na taimakawa wajen kara Kwarin Kashi. Yana kuma taimakawa wajen kara Karfin Hakori, Tsokar Jiki, da Jijiyoyin Jiki. Jikin Mace Mai Juna Biyu na Bukatar Kimanin Milligram Dubu Daya a Kowacce Rana. Ga Mai Juna Biyu Dake da Karancin Shekaru ana bukatar Karin Kimanin Milligram Dari Uku. Dafaffen Alaiyahu, Kifi, Madara ko Yogot da Wasu `Ya`Yan Itatuwa na daga cikin abincin da ke wadata jiki da Wannan Sinadarin.

Harwa yau akwai Sinadarin Bitamin D; Wannan Sinadarin na Aiki a Jiki Tare da Sinadarin Kalshiyom wajen kara Kwarin Kashi da kuma Hakora. Muhimman hanyoyin da ake samun wannan Sinadarai sun hada da Kifi Musamman Salmon, Madara, Kwai da Kuma `Ya`Yan Itatuwa.

Frotin; Mace Mai Juna Biyu na bukatar Sinadarin frotin domin girman abin da ke cikin ta. Mai Juna Biyu na bukatar Kimanin Gram Sabaìn da Daya a Rana. Irinsu Naman Kaza Ko Rago, Akuya, Saniya da sauran Tsuntsaye, Kifi, Kwai, Dangin Wake, Dangin Gyada da Madara.

Sinadarin Ayon; Domin Samun Ishashshen Jini a Jiki da guje wa Ciwon Karancin Jini. Jiki na Bukatar Sinadarin Ayon da Zai Samar da Kwayoyin Jini a Jiki. Mace Mai Juna Biyu na Bukatar Jini Fiye da  Sauran Mata marasa Juna Biyu. Sannan kuma jikin ta na bukatar ayon domin gudanar da jini ga abinda ke ciki. Karancin wannan sinadarin kan Sanya tsananin Ciwon Kai, Gajiya da Kasala ga Mai Juna Biyu. Sannan kuma ciwon Karancin Jini a Jiki kan Kara Hadarin Haifar Jariri Mara Lafiya, wanda Lokacin shi bai kai ba. Haka kuma yana Haifar da Ciwon Damuwa Bayan Haihuwa.

Yawancin wadannan sinadaran na kunshe a cikin magungunan awo na masu juna biyu domin samun wadata. Sannan kuma anfani da abubuwan da zasu wadata su na da muhimmanci sosai.

Domin jiki ya samu damar tatsar wadannan Sinadarai, yana da kyau a hada su da sinadarin Bitamin C. Zaà iya samun sinadarin Bitamin C cikin lemu, ganyayyaki da sauran su.

Ga Masu Fama da wasu nauì na Rashin Lafiya da zai hana su amfani da wasu daga cikin kayan abinci masu anfani, yana da kyau su tuntubi likita domin Shawarwari. Motsa Jiki na da Muhimmanci Wajen Baiwa Jiki Damar tatsar Alfanu Dake Cikin Abinci.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos