Home ยป `Ya`Yan Tafasa (Cassia Seeds)

YaYan Tafasa (Cassia Seeds) Sinadarine da Kasashe da Dama ke Amfani da shi ta Fannoni Daban-Daban. Tun Kaka da Kakanni, ana amfani da shi a matsayin Kayan Miya, Shayi, Shayin Kofi da sauran su. Sannan Kuma Maganine na Larurori Daban-Daban Kamar Matsalar Ciki, Idanu, Ciwon Gabobi, Hanta, Rage Kiba da sauran su. Haka zalika ‘Ya ‘Yan Tafasa suna Daga Cikin Kayan Lambu Da da ake amfani da Ganyen su, Jijiyoyi, Mai, da kuma YaYan su baki daya.

Bincike ya Bayyana alfanun YaYan Tafasa (Cassia Seeds) kamar haka;

 • Magance Matsalar Ido; Sinadarin Retinoyik da ke cikin `ya`yan tafasa ya Sanya ake amfani da shi wajen sarrafa maganin ciwon ido. Yana inganta ganin mutum, kuma ana anfani da shi wajen magance matsaloli da suka shafi ido da dama. Wadannan matsalolin sun hada da Dundumin Ido, Yanar Ido, Hawan Jinin Ido, Kaikayi, Jan Ido, Gani Dishi-Dishi, Bushewar Ido da sauran su.
 • Rage Kiba; amfani da `ya`yan tafasa na hana jiki tatsar sinadarin Kabohaidret da Kitse a cikin jiki. Yana kuma rage yawan ruwa a jiki da kawar da munanan abubuwa da jiki baya bukatar su. Har wa yau yana kone tarin kitse dake cikin jikin mutum. Wannan ke Sanya a samu rage kiba yadda ya dace.
 • Kara Lafiyar Ciki; sinadarin Glaikosit dake cikin `ya`yan tafasa na kara damar tatsar muhimman sinadarai cikin abinci. Wannan na kara lafiyar ciki ta fannain kare shi daga Cushewar, Kumburi da sauran su. Masu fama da ciwon ciki saboda rashin narkewar abinci a cikin ciki kan iya shafa man tafasa a cibiya domin samun sauki.
 • Lafiyar Fata da Gashi; Anfani da tafasa don kara lafiyar fata da Gashi soboda damar yakar kwayoyin cututtuka da yake da shi. Yana kashe kwayoyin cuta ta Bakteriya da Fungus sannan kuma yana hana girman kwayoyin da dama. Ya kan magance cututtukan fata kamar su Kuraje, Kyasbi, Kuturta, Amosani, Makero da sauransu. Shan Garin `ya`yan Tafasa na kare fatar jiki daga kamuwa da cututtuka da dama. Ana amfani da tafasa wajen Sarrafa Hodar Shafawa a fuska.
 • Hawan Jini; ga masu fama da Hawan Jini, amfani da Shayin `ya`yan tafasa a kullum na magance wannan ciwo. Yana kuma Sanya gudanar jini a jiki yadda ya kamata. Sannan yana kare kamuwa da wannan ciwo na Hawan Jini.
 • Lafiyar Zuciya; yanayin da yake da shi na rage sinadarin Kolestrol a Jiki da kuma wadata Lafiyar Zuciya.
 • Mura; Saboda yanayin sa na Kawar da Kwayoyin Cututtuka, amfani da `ya`yan tafasa na kawar da alamomin mura da suka hada da Yoyon Hanci, Tari da Toshewar Hanci. Amfani da man tafasan na taimaka wajen magance Ciwon Kai, Tari, da Yoyon Hanci.
 • Inganta Bacci; Bincike ya nuna cewar amfani da filo wato Matashin Kai da aka sarrafa da `ya`yan tafasa na Sanya samun bacci yadda ya dace. Wannan filo ko matashin kai na kasancewa da dumi a lokcin sanyi ya kuma yi sanyi a lokacin zafi. Haka zalika yana magance matsalar ciwon jiki, jiri, da wasu matsalolin na kwakwalwa.
 • Ciwon Jiki; Shafa man `Ya`yan Tafasa (Cassia Seeds) na magance matsalar amosanin gaba. Sannan kuma yana magance matsalar ciwon jiki. Yana magance matsalar kumburin gaban da inganta gudanar jini a jiki. Ana anfani da jijiyon tafasa wajen magance Harbin maciji, da kuma tsutsar ciki.
 • Laulayin Hakori na yara; amfani da tafasa na magance matsaloli dake tattare da laulayin hakori na yara. Sinadarin Antrakuinon dake ciki na taimakawa wajen kawar da zazzabi, ciwon ciki, gudawa, da ke tattare da laulayin hakori.
 • Yana taimakawa wajen rage gajiya da kasala, saboda muhimman sinadarai dake cikin shi.

Matsalolin dake tattare da anfani da `ya`yan tafasa sun hada da gudawa da matsalolin narkewar abinci a ciki. Ga wadanda ke da wadannan larurori, amfani da `ya`yan tafasa kan zama matsala garesu saboda sinadaran dake ciki ka Iya ingiza su.

Ga masu fama da matsala ta saukan jini wato Low BP, saboda yanayin sa na rage Hawan Jini, zai iya zamo matsala a gare su, ya tsananta saukar jinin.

Mata masu juna biyu su guji amfani da `ya`yan tafasa ba tare da shawarar likita ba. Amfani da shi ka iya taso da nakuda kafin lokaci. Haka zalika masu fama da cutar Karancin Kuzari Jiki.

Sinadaran dake cikin `ya`yan tafasa sun hada da Antiokzidant, kalshiyom, magnishiyom, fotashiyom, zink, Ayon da sauran su.

Idan kana bukatar ingantacciyar rayuwa cikin koshin lafiya, kariya daga cututtuka, ciwon jiki, rage kiba, da samun ingantacciyar lafiyar Ido, Sanya `ya`yan tafasa cikin abubuwan da kake amfani da Su na da Yau da Kullum.

A guji amfani da su fiye da kima na tsawon lokaci domin guje wa illa da zai iya haifar wa.

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos