Home » Gurbatar Muhalli

Muhalli Kamar Yadda Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO Ta Bayyana. Hakkin Kowane a Samar Masa Da Muhalli Da Zai Yi Rayuwa, Koyo Da Koyarwa, Wasa, Aiki Ba Tare Da Wata Matsala Ba.

Gurbacewar Muhalli na da Alaka da Yadda Mutane Suke Rayuwa a cikin sa. Sinadarin Dalma (Lead) Ko Kuma Dukkannin Wata Roba Da Za’a Narka Domin A Sarrafa ta Zuwa Wani Abu na Daga Cikin Abubuwa da ke Gurbata Mana Muhalli. Duk Lokacin da aka Samu Gurbacewar Iska Ko Ruwa a Muhalliinmu  Da Sinadaran Dalma Ko Chemicals. Hakan na Haifar Da Cututtuka Da Suka Hada Da Cutar Sarkewar Numfashi, Ciwon Zuciya, Cutar Daji da kuma Matsalar Kwakwalwa.

Kasashe Na Bakaken Fata da Kuma Masu Matsakaicin Karfi Sune Suke Cikin Hadarin Kamuwa da Matsalolin da ke da alaka da Gurbacewar Muhalli.

Masana Kiwon Lafiyar Muhalli Sun Bayyana Wasu Dokoki Da Za’a Bi Don Rage Gurbacewar Muhalli da Wasu Sinadarai da Zasu Cutar da Iskar Da Muke Shaka, Ruwa Da Muke Sha, Kasa Da Muke Rayuwa Da Kuma Abinci Da Mukeci.

Bincike ya Tabbatar Da Cewa Yanayin Halittar Yara Laakari Da Shekarunsu, Girmansu, Sun fi Shiga Hadari Sakamakon Gurbatar Muhalli. Saboda su Kan Shaki Iska fiye da Babban Mutum Bisa ga Girmansu. Haka zalika Sun fi Manya Cin Abinci Saboda Yanayin Jikin su. Saboda Haka, Kananan Abubuwa Kamar Maganin Kwari ko Sinadarin Dalma Kan Iya Shafar Lafiyarsu Har Tsawon Rayuwarsu.

Sinadarin Dalma a Muhalli; Wannan Sinadarine da ake amfani da shi Wajen Kera Batira ko Fayif na Ruwa. Sai dai Kuma yakan zama Guba ga Al`umma.

Akwai Hadari idan Sinadarin Dalma ya Gauraya Cikin Iska ko ‘Kura idan aka Shaka. Cin Abinci ko Ruwa da ya Gurbata da Wannan Sinadari. Yara Masu Wasa da ‘Kasa ko Fenti Kan Iya Samun Wannan Sinadari.

Wadanda Ke Cikin Hadarin Kamuwa da Cututtukan da ke da alaka da wannan Sinadarin na Dalma Sun Hada da;

Yara Kanana; Saboda Rashin Kwarin Jiki, wannan sinadarin na Dalma na da Matukar Hadari a Garesu. Musamman ma yara da ke Sanya Hannu a Baki ko Kuma Wasu Abubuwan da Suke Wasa da Shi.

Mata Masu Juna Biyu; Ga Mata Masu Juna Biyu, Sinadarin Dalma Dake Yawo Cikin Iska , Ruwa ko Abinci Kan Shafi Dan dake Cikin su. Sannan Kuma Yakan iya Wucewa Cikin Ruwan Nono a Lokacin da Suke Shayarwa.

Manyan Mutane; a Yawancin Lokuta, Manya Sunfi Kusanci da Haduwa da Wannan Sinadari. Sukan yi Rayuwa Da Shi a Wuraren Aikinsu, Gona da Kuma Masu Aiki Cikin Jeji. Sannan kuma sukan ci Karo da Shi Cikin Abinci ko Abin Sha ko Kuma Iska.

Matsalolin da ke Tattare da Shigar Sinadarin Dalma Jiki Sakamakon Gurbacewar Muhalli sun Hada da;

 • Jinkirin Girma Hana Yara Girma
 • Rashin Kaifin Kwakwalwa
 • Rashin Koyar Abu da Wuri
 • Karancin Jini a Jiki
 • Cututtukan Zuciya
 • Rashin Aikin ‘Koda Yadda ya Dace
 • Matsalar Mahaifa
 • Cutar Daji
 • Cutar Sarkewar Numfashi

Wasu Hanyoyin da Zamu bi a Rage Shigar Sinadarin Dalma Cikin Jiki sun Hada da;

 • Kawar da Abubuwan da ke Dauke da Sinadarin Daga inda Yara zasu iya tabawa.
 • Wanke Hannu da Kayan Wasan Yara akai-akai
 • Wankewa, Gogewa Da Sharewa Gidan da kuma Tagogi akai-akai
 • A guji zuwa inda ke da wannan Sinadarin na Dalma

Ba`a Gane Shigar Sinadarin Dalma Cikin Jiki Saboda Babu Wata Alama. Sai Dai Idan Mutum yana shakka, zai iya Tuntubar Likita Domin Gwajin Jini don a Tabbatar.

Kowa na da hakkin samun lafiyayyan muhalli Musamman ma Ruwan Sha. Sai Dai Abin ba Haka Yake ba ga wasu al`umman. Kamar wadan da ke da Sinadarin na Dalma Mai yawa a yankunan su wanda ke sanadiyar Mutuwar Yara Kananan da Dama.

Wannan batu ya kawo ga al`amarin rashin Adalci a Garesu. Masana sun Bayyana cewar ya kamata a samar musu da Wadataccen Kiwon Lafiya da zai Magance Musu Wannan Matsalar. Haka zalika a samar da Hanyar da za`a rage alakar su da wannan guba wato Sinadarin na Dalma.

 

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos