Home ยป Sarkewar Numfashi (Asthma)

Sarkewar Numfashi (Asthma) na faruwa ne a lokacin da Hanyoyin Numfashi suka Toshe ko kuma suka Cunkushe. Ana Samun Numfashi da Kyar, Tari, Atishawa da Cushewar Kirji.

Wannan na faruwa ne lokacin da Tsokar Dake Kewaye da Hanyoyin Jini suka Kame. Sannan Hanyoyin Jinin Zasu Kumbura Kuma zu soma Fidda da Danshi. Hakan ke Haifar da Sarkewar Numfashi.

Wadanda ke da wannan cuta ta Sarkewar Numfashi (Asthma) yawanci na sane da irin magunguna da suke Amfani da su a lokacin da ta tasar musu. Haka zalika ga wanda ya fara samun Cutar a karon farko, yana da Muhimmanci ya Tuntubi Likita da Zarar ya soma samun irin wadannan Alamomin.

Idan ya kasance Mutum na yawan samun sarkewar nunfashin bayan magunguna da yake Amfani da su, wannan na nufin ba ya Amfani da su Bisa Ka’ida. Ko kuma bai Karbe shi ba, yana bukatar ayi masa canji.

Lokacin da wannan cuta ta Tsananta, ana samun alamomi kamar haka; Numfashi Sama-Sama ko Daukewa. Sannan kuma Mutum yakan kasa yin Magana, Tsokar Zuciya kan Makale, Tsananin Zufa da kuma ‘Karuwar alamomin yayin da ya kwanta.

Yana da matukar muhimmanci ga mai cutar Asma da ya lazimci zuwa duba lafiyar sa a asibiti.

Cutar Sarkewar Numfashi Ciwo ne da Ba`a Cika Warkewa Gabadaya ba. Sai dai akan yi Amfani da magunguna domin kawar da alamomin sa. Wannan cuta na tashi ne a lokacin da mutum ya Hadu da wani abin da ke ingiza shi. Wadannan ababen sun hada da ‘Kura, Ra’ba, Kyankyaso, Rashin Karbar wani abu da Jiki ke yi kamar Hatsi, Wasu Kananan Dabbobi Kamar Mage da Sauran su. Sauran sun hada da Mura, da Sauran Larurori da kan shafi Hanci da Wuya. Shan Taba, Tsananin Sanyi da Bushashshiyar Iska, Motsa Jiki, Kornafi, Kasancewar wani Kemikal cikin iska, Shan Wasu Magungunan Rage Radadi, Gajiya da Damuwa.

Wannan na iya tasowa mai dauke da ita a kowanne lokaci. Sannan wasu yanayi kan kara hadarin kamuwa ko tashin wannan cutar. Wadannan sun hada da kasancewa a wurin abubuwa da kan ingiza cutar, rashin shan magani akan lokaci, rashin anfani da shi yadda ya dace, dadewa cikin damuwa da gajiya. Sauran sune, jinya sakamakon Ciwon Suga ko wasu cututtukan da suka shafi hanyoyin Numfashi.

Idan cutar sarkewar Numfashi ta tsananta ba tare da an magance ta ba, ta kan kashe mutum lokaci guda.

Hanyoyin Kariya daga Tasowar Asma sun hada da anfani da magunguna yadda ya dace. Shan magani kafin fita motsa jiki, kare kai daga abubuwa da kan ingiza cutar. A guji shan taba, ko fita waje yayin da ake kura ko tsananin sanyi ko zafi. Wanke hannu a kai a kai, Sanya abin rufe hanci a lokacin da ake shara ko hazo. Wannan cuta na daga cikin cututtuka da ake gado kuma ana iya kamuwa da ita yayin haihuwa ko yanayin rayuwa.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos