Home » Karfin Jima’i

Jima’i Shine Saduwa Tsakanin Mace Da Namiji Ta Hanyar Shigar Da Gaban Namiji (Azzakari) Farjin Mace Wanda Ake Kira Turmi Da Tabarya.

Domin Inganta Jin Dadin Wannan Muamala akwai Bukatar Kula Da Muhimman Abubuwa Dake Kara Jin Dadi Da Kuma Motsa Shaawar Maza Da Mata Da Suka Hada Da Yanayin Abinci Da Muke Ci Yau Da Kullum.

Abinci Na Daya Daga Cikin Abubuwa Dake Kara Da Kuma Jin Dadi Da Motsa Sha’awa a Lokacin Jima’i. Nau`iKan Abincin da Suka Dace Mutane Su Dinga Ci Domin Jin Dadin Jima’i Da Kuma Samun Gamsuwa, Karfin Azzakari, Girman Azzakari, Ni’ima, Karin lafiya Sun Hada da;

Alaiyahu; Ba Kamar Yadda Mutane Ke Tunani ba, Alaiyahu yana Kunshe da Tarin Sinadarai Da Suka Hada Da Mineral, Magniziyom, Iron da suke Taimakawa Wajen Kara Sha`awa,  Kuzari ga Maza, Gamsuwa  Musamman ga Mata.

images (2)

Kankana; Kankana Tana Kunshe da Tarin Sindarin Amino Asit wanda ke Taimakawa wajen Sake Jijiyoyin Jini da Inganta Gudanar Jini a Jiki. Wannnan na Sanya Gudanar Jini a Al`ura Kamar Yadda Maganin Asibiti Viagra Keyi a Jiki.

images (1)

Avokado; Wannan `Dan Itaciya na Kunshe da Sinadarin Faiba, da kuma Lafiyayyen kitse da yake Wadata Jiki da Kuzarin da ake Bukata. Avocado nada Sinadarin Bitamin B6 wanda Masana suka Bayyana Cewar Yana Magance Matsaloli Kamar Gajiya, Kasala, Kumburin Ciki da Sauransu.

images (2)

Strawberry; Na Dauke da Sinadarin Bitamin C dake Inganta Gudanar Jini a Jiki. Sannan Yana Taimakawa Jiki Wajen Samun Sinadarin Okzitosin da aka fi Sani da Sinadarin Kauna Da Yake Motsa Sha’awa Da Jin Dadin Jima’i.

images (3)

Kawa; Daya Daga Cikin Halittun Cikin Ruwa dake da Sinadarai irin su Zink. Sinadarin Zink Na Taimakawa Maza Wajen Kara Yawan Maniyi. Ana iya Samun Sinadarin Zink Cikin `Ya`Yan Kabewa, Kashu, Madara, Nama da Sauransu.

images (4)

Ruman; Tarihi ya Bayyana Wannan `Dan Itaciya a Sawun Gaba Wajen Kara Lafiyar Al`aura (Azzakari) da kuma Inganta Jin Dadin Jima’i. Shan Lemun Ruman na Kara Nishadi, Zagayawar Jini, Motsa Sha`awa da Sauransu. Dukkan Wadannan Abubuwa ne Masu Muhimmanci a Lokacin Jima’i.

Chakuleti; Masana Sun Bayyana Cewar Chakuleti na da Alaka Sosai da Jima’i. Chakuleti Na Dauke da Sinadarin Serotonin dake Sanya Nishadi, Lafiyar Jiki. Yanayin na Farin Ciki  Ko Akasin Haka Na Taka Rawa a Lokacin Jima’i.

Shayin Kwofi; Sinadarin Kafin dake Cikin Coffee na Kara Kuzari. Wannan yana Sa maza Samun Ishashshen Kuzari Lokacin Jima’i. Haka Kuma Sinadarin Caffeine na Magance Matsala da ta Shafi Al`aurar Namiji. Sai Dai Bincike Ya Tabbatar Da Cewa Caffeine yana hana Bacci. Saboda da Haka a Nisanci shan shi a lokacin da ake da Bukatar Bacci.

KOWFI

Gadali; ana amfani da Gadali ne Musamman Domin Neman Haihuwa. Amman bincike ya nuna cewar Jijiyoyin Gadali suna Dauke da Sinadarai dake Motsa Sha`awa. Jin Dadin Jima’i Musamman ga Maza. Yawanci ana Siyar da shi ne a Matsayin Gari, wanda za`a iya Sha Da Madara, Kunu, Hadin Salad, Miya ko Kuma Gasashshen Nama.

Kifi; Kifi Mai Maiko irin Su Salmon, Sardines da sauransu na da sinadarin Omega3. Wannan Sinadarin na Magance Matsalolin Jiki da dama. Kuma Suna Taimakawa Lokacin Jima’i . Za`a iya yin Amfani da Garin Chia ko Jan Algariri Domin Samun Wannan Sinadarai.

Kifi Salmon

Wasu daga cikin abubuwan da ya kamata a Nusan ta dasu domin samun biyan bukata sun hada da.

Shan Giya; Shan Giya Fiye da kima kan Gurgun ta Jima’i. Wannan na da alaka da Illolin Giya da Suke Hana Gudanar Jini a Jiki da Kuma Rage Sinadaran Motsa Sha`awa. Yawan Shan Giya na Sanya Karancin Ruwa a Jikin Mutum. Sannan kuma zaiyi wahala wanda yake cikin maye ya samu Kuzari da Sha`awar Jima’i. Ga Mata takan Haifar da Bushewar Gaba (Farji).

Kitse; Amfani da Kitse Musamman Mara Alfanu a Jiki Kamar Kitsen Nama, Man Shanu, Bota yana Hana Gudanar Jinin Jiki. Yana da Kyau a Guji Cin Abincin da ke da Nama Mai Yawa Saboda yana Sanya wari a Jikin Mutum Musamman Lokacin Jima’i.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply