Home ยป `Ya`yan Itatuwa da ke da Matukar Anfani ga Jiki

Mafi yawan kason mutane basa cike adadin `ya`yan itatuwa da ganyayyakin da ake bukata mutum ya ci a rana. Kaso goma sha biyu cikin dari kadai ke samun wannan adadin a rana.

Bisa ga binciken masana, ana bukatar yayan itatuwa da ganyayyaki su kasance abu mafi girma cikin abincin mu a kullum. Amma a halin yanzu, kaso goma sha biyu ne kawai cikin dari ke sammun wannan dama.

Babu tantama Allah ya albarkaci yayan itatuwa da ganyayyaki da sinadaran faiba, mineral da kuma bitamin masu matukar anfani ga jikin dan adam. Wadannan sinadaran na taimakawa jikin dan adam ya samu kariya daga cututtuka da dama.

Ciwon zuciya, Cutar Daji, cutar damuwa, canjin yanayi da sauransu na daga cikin cututtukan da yin anfani da yayan itatuwa da ganyayyaki ke kare wa.

Yayan itatuwa da suka hada da lemo, mangoro, kankana, inibi da gwanda na da matukar anfani wajen yakar cututtuka a jikin dan adam. Dabino, Ayaba, baure, kankana, tufah, dangin sturoberi, kamar su bluberi suma na da anfani ga lafiya.

Bincike ya tabbatar da cewa anfani da wannan yayan itatuwa babban hanya ce ta yaki da cututtuka da suka shafi zuciya da kuma ciwon suga. Suna kuma taimakawa sosai wajen inganta lafiyar kwakwalwa, kara kaifin tunani da basira.

Har ila yau Bincike ya kara da cewa masu yawan cin wadannan yayan itatuwa basu cika kamuwa da cututtukan zuciya, ciwon daji dama sauran cututtuka.

Nau`in `ya`yan itatuwa da ke da matukar anfani a jikin dan adam sun hada da:

Dabino; wannan nauin abinci ne da ke da zaki da kuma albarka. Cin dabino na rage mummunan kitse a jikin mutum da kuma inganta lafiyar mai ciwon suga. Cin dabino kan sanya koshi ga mai jin yinwa.

images (1)
Dabino

Abokado, wannan Dan itace ne mai maiko. Maikon da ke cikinsa irin na zaitun ne wanda ke da matukar anfani wajen inganta lafiyar zuciya. Wani bincike ya tabbatar da cewa cin abokado ko zaitun a kowacce rana na magance mummunan kiba ko teba.

images (2)
Avocado

Kankana na dauke da ruwa da kuma zaki. Zakin da ke cikin kankana mai anfani ne wanda yawancin yayan itatuwa sun fishi zaki. Shan Kankana na taimakawa wajen rage gajiyan gabobin jiki musamman ga mai motsa jiki.

images (3)
Kankana

Baure nau`i ne na yayan itatuwa wanda ke kunshe da kaso mafi girma na bitamin da jiki ke bukata. Baure na taimakawa wajen inganta baccin mutum, yana taimakawa wajen narkar da abinci da kuma canza yanayin walwalar mutum.

Kiwi (Actinidia chinensis) 1 Luc Viatour
Baure

Ayaba wani abu ne da al`umma ke daukan sa a matsayin abinci mara muhimmanci. Ayaba na kunshe da sinadarai da dama da kuma tarin anfanu cikin jikin mutum.

images (4)
Ayaba

Tufah, Cin Tufah daya a rana na nisanta mutum da likita. Ita tufah na kunshe da sinadaran da ke buda hanyoyin jinin mutum. Wannan babban hanya ce na magance cututtukan da ke da alaka da zuciya.

images (5)
Tufah

Inibi kan taimaka wajen sabunta kwayoyin halittan dan adam. Shan Inibi kan taimaka wajen rage tsufa da yankunewar fatar jikin mutum. Sannan yana rage hadarin kamuwa da ciwon daji kamar su dajin mafitsara, mama, huhu, da na mahaifa. Amma kuma shan inibi yayin da mutumke shan wasu magunguna kan zama illa ga lafiyar dan adam.

images (6)
Inibi

Mongoro kan taimaka wajen inganta lafiyar idanu. Shan mongoro kan taimaka wajen kare mutum daga ciwon dajin ido. Da kuma matsalar zugi a jikin dan adam.

mango fee0d79 e1648560084294
Mangwaro

Yawancin mutane kan nuna damuwar su dangane da suga ko zaki da yayan itatuwa ke dauke da shi. Sai dai wannan zaki ba mai cutar da dan adam bane.

Shan lemun kwalba musamman masu dauke da karin sukari kan zama illa ga mai Amfanin da su.

Ga masu son rage kiba, shan `ya`yan itatuwa kan taimaka wajen ragewa ko kona kitsen jikin dan adam. Yana da kyau mu lazimci shan yayan itatuwa a kammu domin inganta lafiyar jiki baki daya.

Yabintu Abubakar

View all posts

2 comments

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos