Lokacin da mutum ya fuskaci alamomi da ke nuna cewar yana fama da karancin jini a jiki. Yana da Muhimmanci a dauki matakai da zasu magance hakan.
Magance Matsalar Karancin Jini a jiki na da Matakai da Hanyoyi daban-daban Da Yakamata abi.
Hanyoyin magance Karancin Jini a Jiki sun hada da;
- Cin Abinci Mai Dauke da Sinadarin Ayon (Iron); Nau`in abinci masu kunshe da wannan sinadari na taimakawa wajen wadata jiki da jini. Wadannan sun hada da `ya`yan Itatuwa, Koren Ganye, Hantar Kaza da sauran dabbobi, Kwai da sauransu.
- Yawaita cin abincin da ke kunshe da Sinadarin Bitamin C; anfani da Tumaturi, Lemun Zaki da na Tsami, Gwanda, Tattase, Inibi da sauransu. Wannan na taimakawa jiki ya samu damar tatsar sinadarai da zasu taimaka wajen samun ishashshen jini a jiki.
- Bitamin B shima na taimakawa wajen samar da kwayoyin jini a jiki. Ayaba, Bitrut, Brokoli, Gyada da sauran su zasu wadata mutum da wannan sidarai da zasu bada Karfin samun jini.
- Kamar yadda batun yake, Cin Tufa daya ko wacce rana zai kare mutum daga zuwa asibiti. Tufa na Taimako wajen samar da sinadarin Hemogulobin a jiki.
- A guji anfani da Sinadarai da ke hana Jiki Tatsar sinadaran Ayon (Iron) a cikin abincin da muke ci. Shayin Kwofi, Bakin Shayi, Lemon Kolba musamman ma Baki, Giya (Barasa), Goro, Taba, da sauran Lemuka masu dauke da Karin suga.
- Motsa Jiki da Cin Abincin da ya dace; lokacin da mutum ke motsa jiki, jikin na samar da sinadarin Hemogulobin da zai taimaka wajen samar da jini. Sannan cin abincin da ke kunshe da sinadarai masu inganci shine hanya mafi girma wajen wadata na jini.
Binkice ya bayyana wasu daga cikin Nau`in abincin da muke ci na bada gudumawa wajen samun wadatar jini a jiki. Wadannan sun hada da;
- Ayaba; Ayaba na kunshe da sinadarin Ayon (Iron) da sauran Bitamin dake inganta narkewar abinci a ciki. Yana kuma wadata jiki da Jini.
- Danyar Flanten; Itama kamar Ayabar tana wadata jini a jiki.
- Miyar Kubewa; wannan miya na da inganci wajen narkar da abinci da kuma samar da jini.
- Kifi; Yana da sinadarin Frotin da ke da muhimmanci wajen maida jinin da aka rasa sakamakon Haihuwa, Ko Jinin Al`ada, Bada jini, ko Gajiya.
- Miyar Shuwaka (Bitter Leaf); Tana da anfani wajen inganta jini, rage Hawan Jini, Ciwon Suga da kuma wasu cutukan daban.
Akwai wasu nau`ikan Abubuwa da ke da anfani wajen inganta Gudanar jini a jiki. Kuma wadanan na taimakawa wajen inganta Lafiyar Zuciya sosai. Wasu daga ciki sun hada da Tafarnuwa, Albasa, Shambo da sauransu.
- Shambo; Zafin da Shambo ke da shi ya samo asali ne daga sinadarin da ke taimakawa wajen rage Hawan Jini, Kara Karfi da bude Hanyoyin Jini, Wanke Kitse daga Hanyoyin wanda zai bada damar gudanar jini yadda ya dace.
- Albasa; Albasa na dauke da Sinadarin Antiokzidant wanda ke inganta lafiyar zuciya, Bude Hanyoyin Jini, da samar da gudanar jini a jiki yadda ya kamata.
- Tafarnuwa; Itama na dauke da Sinadarin Solfo wanda ke sake hanyoyin jini domin ya samu damar gudana. Bincike ya nuna anfani da tafarnuwa na taimakawa wajen rage hawan jini da kuma sake dukkan jijiyoyi da kuma hanyoyin jini a jiki.
- Citta; yawancin mutanen da ke anfani da citta basu cika kamuwa da matsala ta Zuciya da kuma hawan jini ba.
- Girfa, Bitrut, Kifi, Kurkum, Tumaturi, Lemo da Koren Ganye duka na da anfani wajen buda hanyoyin jini, rage hawan jini da kuma inganta gudanar jinin jiki.
Inganta gudanar Jinin Jiki na da anfani wajen magance matsalar karancin jini a jikin dan adam.
Ga mai fama da Karancin Jini da kuma SAUKAN JINI (Low BP), ya kamata ya mai da hankali wajen anfani da dukkan abin da ke inganta Jinin Jiki masu rage Hawan jini (High BP) a lokaci guda. Anfani da wadannan kan zamo hadari ga rayuwa.
Add comment