Home ยป Ganyen Alobera (Aloe-Vera)

Ganyen Alobera na Daga Cikin Korayen Ganye mai dauke da ruwa mai yauki a cikin sa. Dandanon sa na da Daci a baki. Amma tana kunshe da tarin anfani ga lafiyar dan adam. Ruwan dake cikin wannan ganye na da alfanu da dama.

Tarihi ya nuna cewa ana anfani da wannan ganye shekaru da dama a matsayin wani nau`in sinadari a cikin abinci. Sannan kuma ana anfani da shi a kayan kwalliya, magunguna da sauransu.

Bincike ya bayyana wasu hanyoyin da ake Amfani da Wannan Ganyen. Ganyen Alobera na kunshe da sinadarin Bitamin C wanda ke taimakawa wajen Yakar Cututtuka. Bitamin C na kare mutum daga kamuwa da cututtukan zuciya. Sannan wadatar shi a jiki kan Sanya tatsar wasu sinadarai masu anfani ga jiki cikin abincin da muke ci.

  1. Hakori da Dadashi; Sanya ganyen alobera cikin man goge baki na taimakawa wajen yakar ramukan Hakora. Yana kashe kwayoyin Bakteria na cikin baki fiye da mafi yawan man goge hakora.
  2. Kumburin Ciki: Bisa ga Binciken da aka Gudanar, Shan Kimanin akalla Milligram 50 zuwa 200 na wannan Ruwan Ganyen na tsawon Kwanaki 10 zai magance matsalar kumburin ciki.
  1. Maganin Gyanbon Ciki (Ulcer): Ga Wadanda ke fama da wannan ciwo anfani da Alobera kan magance wannan matsala. Yana Sanya samun wadatar ruwa a jiki.
  1. Fatar Jiki: Ana anfani da Ruwan da furen wannan ganye a Fatar Jiki Domin warkar da Yanka ko Gurjewa a Jiki. Aloe-Vera Tana magance yankwanewar fata da rage tsufa. Domin tana kara sinadarin kolajin a jiki. Tana rage Bushewar Fata, Kawar da Kyasbi, Kuraje da sauran Cututtukan Fata.
  1. Kariya Daga Kunan Zafin Rana: Bincike ya nuna cewar Kananan Ganyayyaki na Alobera wadanda basu fi sati da fitowa ba na maganin Kunan Zafin Rana a jiki fiye da manyan ganyen. Sai dai suma manyan na da nasu anfanin. Haka zalika yana da anfani ga wadanda akayi wa aiki na gashi a Asibitoci Domin Kare Lafiyar Fatar su. Wannan ganye na dauke da sinadaran Bitamin, Mineral, Amino Asit da Antiokzidant.
  1. Rage Damuwa da Kara Kaifin Basira: Masana sun nuna Cewar anfani da wannan ganye na taimakawa wajen kara kaifin Basira da Kuma Rage Damuwa da Kaso mai Girma.
  1. Warkar da Ciwon Kunan Wuta: An gudanar da bincike tsakanin maganin da ake shafawa kunan wuta a asibiti da kuma Ruwan Alobera. Wannan ya bayyana alobera yafi warkar da ciwon da wuri fiye da maganin na asibiti.
  1. Rage Hawan Jini: Yana Taimakawa Wajen Rage Hawan Jini wanda ke da alaka da Ciwon Suga.
  1. Gyara Gashi:bisa ga yanayi da wannan ganye ke da shi na Sanya Danshi. Ana anfani da shi a Gashi Domin Hana Kaikayi, Bushewar Gashi, da kuma Amosanin Gashin. Wannan zai Sanya Girman Gashin ba Tare da Karyewa ba.

Ana anfani da Ruwan Alobera a Danyen sa a Lokacin da aka tsinka. Ko kuma wanda aka Sarrafa. Sannan ana iya markada shi a ayi anfani da shi.

Dukkan binciken sun bayyana cewa, yana da muhimmanci a gwada a wani Shi a wani Sashen Jiki kadan domin gudun Borin Jini. Duk da tarin alfanu da wannan ganye ke da shi, yana kuma da wasu illoli a wani Lokacin.

Bisa ga yanayin Daci da yake da shi, shan shi da yawa kan Sanya samun matsala ga Hantar Mutum. Sannan a lokacin da ake anfani da shi a gida kai Tsaye, baza a iya cire wasu daga cikin abubuwan da kan zamo illa ga jikin mutum ba. Yana da muhimmanci a tuntubi likita kafin ayi anfani da wannan ganye na Alobera a ko da yaushe. Sannan idan aka fuskanci wani canjin yanayi lokacin da ake anfani da shi, a dakatar da anfani da shi sannan a tuntubi likita.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply