Home » Ruwa

Ruwa Ginshikin Rayuwa. Ruwa Abokin Rayuwa. Kaso mafi girma na Jikin dan adam ruwa ne. Hakan yasa, yake da matukar muhimmanci mutum ya kasance cikin shan ruwa ako da yaushe.

Sanin iya adadin ruwa da mutum ya kamata ya sha na Rikitarwa. Wani lokacin yana da Wuyar Ganewa, Musamman a lokacin da ake tsananin zafi ko kuma Sanyi. Saboda gujewa Karancin Ruwa a Jiki ko kuma yawan shi a jiki.

Hukumar Lafiya ta bada shawarar shan kimanin kofi 6 zuwa 8 a rana. Amma kuma binciken makarantar kimiya ta Amerika ta bayyana cewar kimanin kofi goma sha biyar da rabi ga maza. Sannan kuma su mata, kimanin kofi goma sha daya da rabi a rana. Amma dai wannan adadin ya kunshi ruwa da kuma sauran ababen sha da kuma Koren Ganye.

Wannan adadin ruwan ya danganta ne da yanayin da ake ciki zafi ko sanyi. Masana sun bayyana cewar duk wanda ke aikin karfi ko kuma motsa jiki na bukatar shan ruwa kafin, da Kuma bayan lokacin da yake gudanar da aikin. Wannan ya hada da dukkan aikin da ya shafi karfi ko kuma zubar da gumi.

Yawan gumi kan sanya rasa ruwan jiki. Saboda haka, ya zama dole ga masu zama a yankunan da ke da yawan zafi kamar masu zama a yankunan duwatsu da su lazimci shan ruwa.

Masana sun gano cewar Zazzabi, Amai, da Gudawa kan sanya a rasa ruwan jiki. Hakan ya sanya shan ruwan mutane marasa lafiya ke karuwa. Wasu cututtuka kamar cutar Mafitsara na sanya yawan shan ruwa.

Yawan jin kishin ruwa, Yin Koren Fitsari Mai Wari na daga cikin wasu alamomin rashin ishashshen ruwa a jiki. Wasu alamomin sun hada da Bushewar Lebba, Rashin Nauyin Jiki da Jin Jiri.

Shan Ruwa, Madara, Shayi, ko Lemo na daga cikin hanyoyin samun wadatar ruwa a jiki. Amma yana da kyau a kula da yawan shan suga sabo da hadari ne ga lafiyar dan adam.

Ba wata matsala bace idan mutum bai cika jin kishin ruwa ba, idan har fitsarin mutum bai canza launi ba kuma babu wani damuwa da yake ji.

Akwai yuwuwar mutum ya sha ruwa fiye da yadda jiki ke bukata. Amma ba matsala bane idan har wanna mutumin bashida Matsalar Koda. Sai dai a wani lokacin yakan iya haifar da yanayi na taruwar ruwa a jiki. A wannan yanayi, likitoci kan bada magungunan da ke Sanya yawan jin fitsari don rage wannan Ruwan.

 

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos