Home ยป Dundumin Ido

Dundumin Ido wanda ake Kira Night Blindness a turance matsala ce ta ido. Wannan matsalar na Sanya rashin gani cikin dare a inda babu haske sosai ga masu fama da ita.

Ana kamuwa da wannan matsalar ne a lokacin da wani sashe na ido da ake kira retina ya daina gudanar da aiki yadda ya dace. Ko kuma a wani sa`in idan ta daina aiki baki daya. Wannan na faruwa ne bisa ga dalilai daban-daban.

Dalilan da ke Haifar da Kamuwa da Dundumin Ido sun hada da Yanar Ido, Hawan Jinin Ido, Ciwon Suga, `Karin Ido, Ciwon Rashin Gani Daga Nesa, da sauran su. Akan iya samun wannan Larura tun daga Haihuwa ko kuma Gado daga cikin Dangi.

Karancin Sinadarin Bitamin A Cikin Jikin Mutum na Sanya Kamuwa da Wannan Larura. Bitamin A na daga Cikin Manyan Sinadarai da ke Inganta Ganin Mutum.

Ciwon Suga Bashi da alaka ta Kai Tsaye da Wannan Larura. Amma ya kan Haifar da Karancin Wasu Sinadaran da Zasu Sanya a samu wannan larurar. Gudanar da aiki (tiyata) a ido idan ba`a dace ba kan Haifar da wannan larura ta Dundumi.

Idan wannan larurar ta samo asali ne daga dangi, bisa ga wasu cututtukan da ake gado, ta na iya janyo rashin gani yadda ya dace ko da da rana ne. Ta kan Sanya yawan motsin ido ba tare da mutum ya sani ba, ko wadanda idanun ke nuna alamun Kallon wani wuri yayin da suke Kallon wani wuri daban Wato harara garke.

Wasu daga cikin magungunan Cutar Hawan Jinin ido na iya janyo larurar Rashin gani cikin dare. Ko kuma yawan canje-canjen magungunan idon.

Alamomin wannan larura ta Dundumin Ido sun hada da rashin gani sosai a wurin da babu haske cikin dare. Sannan akwai rashin iya tuki cikin dare, rashin iya gane mutane, gani dishi-dishi idan aka samu haske lokaci guda da sauran su.

Likitoci kadai ke iya tantance wannan larura ta Rashin gani cikin dare (Dundumi). Saboda haka, yana da muhimmanci a tuntubi likita a lokacin da ake da wata matsala ta gani.

Magance wannan matsala ta kunshi binciko musabbabin kamuwa da ita. Idan masana suka fuskanci larurar na da alaka da rashin muhimman sinadarai a jiki, to samun wadatar wadannan sinadaran kan samar da sauki.

Wasu daga cikin cututtukan ido kamar su Yanar Ido na bukatar a gudanar da aiki (tiyata) domin a cire su.

Ana samun saukin wasu daga cikin larurar wanda aka gada ta hanyar anfani da tabarau masu kunshe da magani.

A yawancin lokuta, anfani da abubuwa masu dauke da sinadarin Bitamin A na taimakawa sosai. Yana da muhimmanci a lura da lafiyar idanu ga mai dauke da larurar ko mara shi. Zuwa asibiti akai-akai domin duba lafiyar idanu zai taimaka a gane idan mutum ya kamu da larura a kan lokaci.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply