Home ยป Aya (Tiger Nuts)

Aya (Tiger Nuts) na daga cikin abincin da ake samu daga Jijiyoyin Ciyayi. Duk da cewar tana kama da su gyada, amma bata daga cikin dangin gyada. A wasu kasashe, aya tana a matsayi ne na Ciyawa Kawai. Wasu Kuma na Amfani da ita Wajen Ciyar da Dabbobi su.

Yawancin Mutane suna Sarrafa Aya Ta Hanyoyi Daban-Daban Da Suka Hada Da Aya Maisuga, Aya Maigishiri, Jikakkiyar Aya Ko a Sarrafa Da Gyada Don A Samar Da Damuwa Ko Kuma Ayi Wato Kunu Da Ita Wanda Ake Kira Kunun Aya.

Aya na Dauke da Muhimman Alfanu ga Lafiyar Jikin Dan Adam Da Suka Hada Da:

Kara lafiyar Zuciya, Aya na Kare Mutane Daga Kamuwa Da Ciwon Suga, Ciwon Hawan Jini, Rage Kiba, Kara Kuzari, Kara Ni`ima ga Mata, Kara Lafiyar Ciki, da Inganta Garkuwar Jiki.

Sinadaran da ke cikin Aya ya Sanya ta zamo abu mafi inganci wajen inganta Mu`amala ta aure. Hakan ya Kasance ne Sakamakon Kara Kuzari da take yi Ga Maza da Mata. Sannan kuma tana inganta Kwayoyin Halittar Da Namiji.

Aya tana dauke da Sinadarin Antiokzidant wanda ke taimakawa jiki wajen kare Shi daga tsufa. Wannan na nufin yana sabunta kwayoyin halittan mutum. Haka zalika, tana da Bitamin E dake kare jiki daga cututtuka. Bitamin C dake cikin ta kan Sanya ciwo warkewa da wuri da kuma kara lafiyar fatar jiki.

Aya tana kunshe da sinadarin Faiba wanda ke taimakawa wajen cire dukkan Karin sinadaran da jiki baya bukatar su. Faiba na hana mutum Jin Yunwa, Inganta Lafiyar Ciki, Lafiyar Zuciya, Rage Kiba, da Kare Cutar Suga a Jiki.

Wannan muhimmin abinci wato Aya na da alfanu wajen yakar kwayoyin Bakteria a jiki. Tana da Muhimmanci Wajen Magance Matsalar da Cutar bacteria ke Janyowa Musamman wanda yaki jin Maganin Asibiti. Har wa yau yana inganta Garkuwar Jikin Dan Adam ta hana shi kamuwa da cututtuka.

Sinadarin Magnishiyom na cikin Aya na Kara Karfi ga Jijiyoyi da Tsoka na Jikin Mutum. Yakan taimaka wajen inganta aiyukan su yadda ya dace. Fotashiyom na taimakawa wajen kare cutar Hawan Jini, Ayon na kara kwayoyin jini a jiki da kare mutum daga cutar karancin jini.

Sinadarin Kalshiyom dake cikin Aya na kara karfin kashi, anfani da shi na kare mutum daga cutar rashin kwarin kashi.

Bincike ya nuna cewar ba`a cika samun damuwa daga anfani da Aya ba. sai dai yana da muhimmanci a kiyaye yin Amfani da ita fiye da kima.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos