Zafi Wani Yanayi ne da yake cike da wasu abubuwa dake barazana ga lafiyar al`umma. Azumi cikin Yanayin zafi na da matukar wahala ga masu yin sa. Wani lokaci masu fama da rashin lafiya sun fi shiga damuwa a wannan yanayi.
Haka kuma Al`umma na shiga yanayi na damuwa da kuma rasa inda za`a saka kai saboda zafi. A wannan yanayin azumi kan sa ba a samun damar shan ruwa domin jin saukin yanayin na zafi.

Lokacin zafi a na bukatar a sha wadataccen ruwa domin lafiyar jiki. Masana sun bayyana cewa, yayan itatuwa kamar su kankana, gurji, tumaturi da ganyayyaki suna taimakawa wajen dawo da Ruwan jiki.
Likitocin sun kara da cewa ci ko shan wadannan kayan abinci ko da daddare ne zai taimaka wajen kare lafiyar mai Azumi. Zai kuma wadata jikin mai azumin da adadin Ruwan da yake bukata.

Bincike ya nuna cewar, Galibin cuttutuka sunfi tashi a lokacin damuna da kuma zafi. Don haka ya kamata mu kiyaye mu kula da lafiyar mu. A daya bangaren kuma lokacin azumi a na bukatar kulawa sosai musamman ta bangaren lafiya.
Yana da muhimmanci mu kula da fadakarwan likitoci da masana kiwon lafiya. Kimanta cin abinci, sannan a kuma cike su da yayan itatuwa da kuma ganyayyaki, wannan zai taimaka wa lafiyar mai Azumi cikin yanayin zafi.

Azumi ibada ce ta musamman. Wannan yanani na zafi yana da kyau mu kula da yanayin rayuwa, abincin mu da abun sha, mu guji aikin da zai kawo gajiya sosai. Mu kiyaye shaye – shaye, Sannan kada mu zama masu son jiki don inganta lafiyar mu baki daya.

Masha Allah
Madalla da Waraka