Home ยป Lafiyar Mai Azumi

A lokaci da Mutum ya soma Azumi, Jikin Mutum na fuskantar sauyi da dama. Wani lokaci yawancin mutane na da dabiar rashin karyawa da safe, Wannan shima nau`i ne da jiki ke shiga mai kama da na azumi.

20240311 151243
Lokacin Bude Baki A Jihar Kano

Wasu daga cikin dalilan da muta ne ke yin azumi sun hada da; na farko Ibada. Sannan ana yin azumi bisa wasu dailai kamar, rage kiba, kara kaifin basira da kuma tsawon rayuwa.

Yin azumi na da anfanu da dama ga lafiya da rayuwar jikin dan adam. Wadannan anfanun sun hada da rage mummunan kiba ko teba. Lokacin da mutum ke jin yinwa, jikin sa na samar da hanyar da zai ci gaba da gudanar da aiki. Saboda haka, Jikin zai yi anfani da kitse da ya tara na baya. Wannan zai taimaka wa jiki ya samu sinadaran da Jiki yake bukata kuma ya narkar da sauran.

20240311 163520
Lokacin Bude Baki A Jihar Borno

Haka zalika, a lokacin da mutum ke azumi, kwakwalwar sa tafi kaifi domin adadin suga dake cikin jikin mutum na raguwa. Raguwar sugar ke sanya ya samu nutsuwa sosai.

Har wa yau, Bincike ya nuna cewa, jin marmari ko kwadayin abinci ko abin sha hanya ce da zai taimaka mutum ya ci abinci sosai. Zai bada damar samar da adadin sinadaran da jikin ke bukata a lokacin da aka ci abinci.

20240311 163740
Lokacin Bude Baki A Jihar Lagos

Yana da muhimmanci a kula da motsa jiki. Shi zai taimaka wajen tatsan sinadaran da ke cikin abincin da mutum ke ci. A wasu mutane, yin azumi kan taimaka wajen samar da sinadaren da zai taimaka wajen daidaita jinin jikin dan adam.

Hakan Yana taimakawa wajen sabonta kwayoyin halittan mutum wadanda su ka tsufa. wata hanya ce ta inganta Lafiyar Mai Azumi.

Azumi na warkar da cututtuka da dama wanda har yanzu Binciken kimiyya bai iya gano adadin cutukan ba.

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos