Home » A SAMARWA DA YAN NAJERIYA MAGANIN ZAZZABIN CIZON SAURO KYAUTA – MAJALISA

A SAMARWA DA YAN NAJERIYA MAGUNGUNAN ZAZZABIN CIZON SAURO KYAUTA – Majalisar Wakilai


Majalisar Wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta yin amfani da wani bangare na kudaden da aka samu daga cire tallafin man fetur domin samar da maganin zazzabin cizon sauro kyauta a dukkan asibitocin gwamnati a Najeriya. Ta kuma bukaci ma’aikatar lafiya da ta samar da wadansu bangarori a cikin dukkan asibitocin gwamnati da Za’a dinga karbar wadannan magunguna kyauta.

A zaman na majalisar ta bayyana cewa idan ba a kula da shi ba, zazzabin na Maleriya na iya haifar da munanan matsalolin lafiya kamar, lalata kwakwalwa, matsalar numfashi, raunin gabobi har ma da rasa rayuwa baki daya.

A cewar majalisar, matsakaicin farashin maganin zazzabin cizon sauro a Najeriya a yau ya kai kusan N5,000.00 banda kudin gwaje-gwajen dakunan gwaje-gwaje, idan kuma ma har da kudin gwaje-gwajen adadin na iya kaiwa sama da N10,000.00.
Inda majalisar ta bayyana cewa “Yanzu da yawa ‘yan Najeriya ba sa iya biyan wadannan kudade. Saboda haka, suke yin amfani da ganyayen gida ko magunguna marasa inganci waɗanda za su iya rikita cutar har ta kai ga rasa rayuwar marar lafiyar.”

A karshe majalisar ta bayyana damuwarta kan yadda halin da kasa ke ciki a halin yanzu, inda abinci daya a kowace rana ke da wuya ga mafi yawan talakawa da masu karamin karfi da tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur, wanda hakan ya sanya samun damar sayan magungunan zazzabin cizon sauron ya zama abu mai matukar wahala, a don haka akwai bukatar gwamnati ta sa baki wajen samar da maganin zazzabin cizon sauro kyauta a dukkan asibitocin gwamnati.

Umar Abubakar Imam

View all posts

Add comment

Leave a Reply