Home » A Duk Mintuna Biyu Yaro Guda Na Mutuwa Sakamakon Zazzabin Cizon Sauro

A DUK CIKIN MINTUNA BIYU YARO DAYA NA MUTUWA SAKAMAKON CUTAR ZAZZABIN CIZON SAURO – WHO


Sauro mugun iri, Lange Lange mai ramar ƙeta. Cutar zazzabin cizon sauro Itace ta uku a duniya da ta fi kashe kananan yara yan kasa da shekara biyar.

A shekarar 2019, yara yan kasa da Shekara biyar kimanin 274,000 ne suka mutu sakamakon cutar Maleriya, wanda yawan adadin ya kai kaso 67 cikin 100 na mace-macen a sakamakon cutar a fadin duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta Bayyana cewa a Kowanne minti biyu, yaro daya yana mutuwa sakamakon zazzabin da sauro ke haifarwa.

Kawar da wannan cuta mai matukar hadari da sauro ke haifarwa na bukatar karuwar zuba jari a duniya musamman wajen yin bincike da kuma Gangamin wayar da kai a kafafen yada labarai.

Domin kaucewa Kamuwa da Cutar ta Zazzabin Cizon Sauro Waraka Media Concepts Development Hub na kira ga Al’umma da su rika Amfani da gidan sauro mai dauke da maganin kashe kwari wato insecticide mosquito net.

Duba da cewa hanya daya tilo ta samun kariya daga wannan cuta itache gujewa haduwa da sauro ta kowane hali.

Zama Da Lafiya Ya fi zama da Abinci a Rumbu inji masu iya magana.

 

Umar Abubakar Imam

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos