Home » RASHIN BIN KA’IDAR MAGANIN TAZARAR HAIHUWA NA SA MACE YAWAN ZUBAR DA JINI

RASHIN BIN KA’IDAR MAGUNGUNAN TAZARAR HAIHUWA NA SA MACE YAWAN ZUBAR DA JINI – DR. UMMILKHAIRI IBRAHIM HASSAN


Likitoci da dama na cigaba da bayanai da kuma wayar da Kai game da yadda mata zasu kula da kansu Musamman Idan mace tana kan bin tsarin bada tazarar haihuwa, wajan kaucewa matsalolin da akan fuskanta a wasu lokutan matukar ba’a bi ka’idar da aka shimfida.

Kamar dai yadda muka samu zantawa da wata kwararriyar likita dake aiki a asibitin sir Muhammad sunusi anan jahar kano, ta bayyana mana cewar matukar mace tabi wannan tsarin na bada tazarar iyali, to ya zama wajibi ta kasance tana tsaftace jikin ta fiye da yadda take a baya, domin kaucewa kananan cututtukan da za’a Iya kamuwa dasu a lokacin, domin kuwa garkuwar mace a wannan lokacin ta kan yi rauni, Kamar dai mai juna biyu, hattama Irin laulaye laulayen nasu kan zo daya, Sai dai ita mai ciki nata yakan tsananta ta wasu hanyoyin daban.

Dr Ummulkhairi Ibrahim Hassan, ta kuma ce yana da kyau mace tabi shawarwari da tsarukan da aka shimfida mata a lokacin da ta ziyarci asibitin, kuma sannan ya kasance ana bin su a aikace kamar yadda aka tsara musu.

Kazalika ta kuma kara da cewa, rashin bin hakan kan haifarwa da matan matsalar yawan zubar jini wanda da dama su ke kokawa, Musamman Idan mace akan bin tsarin shan kwaya take kuma bata bi lokacin da take sha ba har ya wuce ta, haka itama wacce ta sadu da mijinta bayan gama al’ada kuma bata san daukar ciki a wannan lokacin, matukar dai itama tasha kwayar nan ta agaji har tsawan kwanaki uku a jere, ko da kuwa a rarrabe ne, Idan dai har ta aikata hakan sau uku kuma duk tasha kwayar, to babu shakka hakan kan sa yawaitar zubar jini ga mata.

A karshe dai likitan taja hankalin mata dasu fara neman amincewar mazajan nasu kafin su zo, da kuma dagewa wajan ziyartar asibiti akai akai ba sai anji tasowar matsala ba, kuma a dinga tambaya game da abinda ya shige duhu domin gano ta yadda zasu shawo kan matsalar da take tattare dasu.

Umar Abubakar Imam

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos