Home ยป ZAZZABIN TAIFOT (Typhoid Fever)

Zazzabin Taifot Dai Cuta Ce da ake Yawan Samu a Kasashe Masu Tasowa. Kwayoyin Cuta Na Bakteria Suke yada wannan cuta. Sannan an fi samun ta cikin ruwa ko abinci mara tsafta. Hakan yasa wannan cuta bata da yawa a wurare da aka tsaftace Ruwan shan su da kuma kayan abinci.

Nahiyar Afrika da kuma Asia na da kaso mafi girma na wannan cuta ta Zazabin Taifot wanda kuma yake sanadin kashe mutane da dama musamman yara kanana.

Anfani da abinci ko ruwa dake dauke da kwayoyin wannan cutar kan sa mutum ya kamu da ita. Haka zalika mu`amala ta kusanci da mai dauke da wannan cuta kan sa a kamu da cutar.

Zazzabin Taifot na sanya mutum ya Kamu da ciwon kai, ciwon ciki, kunburin ciki ko gudawa bayan shi Zazzabin kanshi. Shan magunguna kashe wannan kwayoyin cuta na sa mutum ya samu sauki cikin kwanaki bakwai. Amma idan ba`a magance shi ba, ya kan tsananta har ma ya kai ga kisa.

Alamomin Zazzabin Taifot na fara bayyana daga sati na farko daga kamuwa da cutar zuwa sati uku. Sannan alamomin sun banbanta cikin mutane.

Yawanci akan fara Samun Zazzabi wanda a hankali kan yi Tsanani. Jin Sanyi, Gajiya da Kasala, Ciwon Jiki, Ciwon Ciki, Kunburin Ciki, Gudawa da Kuma Fesowar Kuraje a Jiki. A wani sa`in wasu na kamuwa da Tari, Rashin Son cin Abinci da Kunburin Jiki.

A lokacin da wannan cuta ta soma tsananta, kumburin cikin na karuwa sosai, zafin ciki, da yaduwar cutar a dukkan gabobin jiki baki daya. Tsanantar cutar kan Sanya gushewar hankali har ta kai ga mutuwa.

Mutane na daukar wannan cutar a lokacin da wasu ke da cutar a kusa. Cin abinci ko anfani da Ruwan da ke dauke da kwayoyin cutar na sa akamu da ita. Kyayoyin wannan cuta na fita ta hanyar bahaya ko kuma fitsarin mai dauke da cutar. Rashin wanke hannu akai-akai kan zamo silar kamuwa da cutar.

Yawanci yin bahaya ko bawali a fili ko kusa da ruwa kan sa mutanen da ke yankin kamuwa da cutar. Ko da ba`ayi anfani da ruwan kai tsaye ba, kayan lambu ko yayan itatuwa na Kwaso su idan aka yi anfani dasu ba tare da sun dahu sosai ba.

Yin anfani da kankara ta irin wannan ruwa, ko lemo kan Sanya mutum cikin hadarin kamuwa da cutar ta Taifot.

Tsanantar Zazzabin Taifot

Lokacin da wannan cuta ta tsananta, ta kan haifar da kuraje cikin hanji, zubar jini dama hujewar hanjin. Wannnan zai Sanya bahaya ta dinga zuba cikin cikin mutum. Haka zalika ta kan Sanya tsananin ciwon ciki da amai sakamokon wannan dama tsagewar hanji.

Cutar Taifot bata tsaya nan ba, takan haifar da ciwon zuciya, kumburin hanyoyin jini, koda, mafitsara, madaciya da ma shafar kashin gadon bayan mutum. Haka zalika, tsanantar cutar kan Sanya samun damuwan kwakwalwa.

Hanyoyin kariya daga cutar Zazzabin Taifot sun hada yawan wanke hannu. Hannu Shine gaba da aka fiye yawan mu`amala da aiyuka a jikin mutum. Wanke Hannu akai-akai kan taimaka da rage kwayoyin cuta daga shiga cikin jiki.

Anfani da tsaftaceccen ruwa wata hanya ce ta kariya daga cutar. Tafasa ruwa da tace sa a yayin da ake zargin gurbatacce ne. Ga mai hali za`a iya anfani da ruwan roba ko kuma na leda da aka tabbatar da ingancin sa.

A dafa abinci sosai ya nuna kafin ayi anfani da shi. Ganyayyaki da yayan itakuwa kuma a tabbatar an wanke su da tsaftaceccen ruwa da kuma gishiri kafin ayi anfani da su. Cin abinci da zafin shi zai taimaka.

Koya wa yara kanana tsafta na da matukar anfani domin kare su da kuma iyalai daga kamuwa da cutar Zazzabin Taifot.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos