Home » Ranar Gangamin Kan Shanyewar Ɓarin Jiki Ta Duniya 2023

Hukumar Lafiya ta Duniya ce ta ayyana duk ranar 29 ga watan Oktoban kowace shekara domin gangamin wayar da kan al’ummar duniya game da larurar shanyewar ɓarin jiki da kuma yi wa hukumomi, likitoci da manazarta ƙaimi domin himmatuwa wajen samo nagartattun hanyoyin da za su kyautata rayuwar masu fama da larurar.

Haka kuma, muhimman saƙonnin ranar suna mai da hankali wajen fayyace matakan kariya daga larurar.

Taken ranar na bana shi ne ” haɗa ƙarfi domin galaba kan shanyewar ɓarin jiki”. Wannan take kira ne ga al’umma kan muhimmancin haɗa ƙarfi da ƙarfe domin kiyaye afkuwar shanyewar ɓarin jiki.

Wannan cuta ta shanyewar ɓarin jiki da ake kira da “brain stroke” a turance, wanda aka fi sani da ciwon faralayis (paralysis) na faruwa ne sakamakon katsewar jinin da ke kai wa ƙwaƙwalwa iskar oksijin da sinadarin gulukos, hakan na faruwa idan jijiyar jini a ƙwaƙwalwa ta fashe ko kuma ta toshe.

Hukumar lafiya ta duniya ta ayyana cewa a kowace shekara mutum miliyan 15 ne ke samun wannan cuta, kuma daga cikinsu mutum miliyan biyar ne ke mutuwa nan take ko bayan wani lokaci sakamakon cutar, wata miliyan biyar ɗin kuma su rayu amma su ƙare rayuwarsu da sauran nakasu a sassan jikinsu, sannan ragowar miliyan biyar ɗin ƙarshe su warke sumul kamar ba su yi cutar ba.

Mutanen da ke da haɗarin kamuwa da wannan cuta sun haɗa da:

1) Masu hawan jini,

2) Masu ciwon siga,

3) Mashaya taba-sigari,

4) Masu ciwon sikila (amosanin jini),

5) Masu tararren kitse a cikin jini,

6) Masu ƙiba ko teɓa,

7) Mashay giya / barasa,

8) Masu ciwon zuciya,

9) Masu ɗabi’ar ƙin motsa jiki,

10) Masu shekaru fiye da 30, da dai sauransu.

Alamun da ke nuna mutum ya kamuwa da wannan cuta sun hada da:

1) matsananci ciwon kai,

2) hajijiya / juwa,

3) nauyi ko sagewar ɓarin jiki

4) karkacewar baki / fuska musamman ga masu hawan jini ko ciwon siga,

5) Fitar hankali tare da faɗuwa kwatsam.

Alamun kamuwa da shanyewar ɓarin jiki sun haɗa da:

1) shanyewar ko raunin ɓarin jiki, hagu ko dama, wani lokacin duka biyun,

2) fitar hankali ko suma,

3) amai,

4) ɗaukewar, nauyi ko sarƙewar magana,

5) karkacewar baki, da sauransu.

Ga waɗanda hankalinsu bai fita ba a lokacin afkuwar wannan cuta su kan bayar da rahoton matsanancin ciwon kai dab da faruwar abin, gani dishi-dishi ko garara-garara, da dai sauransu.

Wannan cuta tana zuwa ne kamar mutuwa, ana tafe, ana zaune, ana aiki, ana farke ko ana bacci. A duk lokacin da wani ya samu wannan cuta ana matuƙar buƙatar garzayawa da shi asibiti a cikin awanni uku da faruwar matsalar, saboda yawan jinkirin da aka yi a gida ko asibitin da babu ƙwararrun likitoci, to yawan jinkirin da za a samu kenan wajen warkewa.

Daga ƙarshe, ga duk wanda ko wani ya samu wannan cuta, yana asibiti ne ko yana gida, sannan ka fahimci cewa daga cikin likitocin da suke duba shi babu likitocin fisiyo (Physiotherapists) to lallai aƙwai buƙatar ya tattauna da likitan kan gayyato likitocin fisiyo domin ci gaba da duba shi kafin matsalolin nakasa su fara bayyana a hannu ko ƙafa.

WorldStrokeDay2023

 

Suwaiba Abdullahi Sarki

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos