Home » Cutar Kyanda


Kyanda cuta ce ta wacce ke yawo a Cikin iska ma’ana cutace da ake Dauka ta hanyar shakar iska ko amfani da wani abu da mai cutar ya taba.

Cutar kyanda na samuwa ne sanadiyyar wata kwayar VIRUS da ake kira MORBILLIVIRUS. Cutar tafi kama Kananan yara A duk lokacin da Aƙalla yara goma suke zaune guri guda tare kuma da wanda ke dauke da cutar, To akwai yiwuwar suma za su iya Kamuwa in har ba’a yi musu rigakafin cutar ba.

Hanyoyin da cutar take yaduwa sun hada da:
Cin Abinci ko Abinsha tare da mai dauke da cutar, Musayar hannu ko rike hannu ko rungumar wanda ke dauke da cutar.

Alamomin cutar kyanda Sun hada da: Zazzabi mai zafi, Yawan gajiya, Tari mai wahalar fita, Idanu suyi Ja, Ciwon hanci, fesowar kuraje a jiki baki daya.

Daga mai juna biyu zuwa ga jaririn ta suna cikin hadarin kamuwa da cutar a lokutan haihuwa ko kuma lokacin da suke shayarwa, shakar numfashin wanda ke da cutar na iya sa a kamu da cutar.

Daga cikin illolin wannan cuta akwai;
Cutar takan sa Ciwon kunne, Namoniya, kumburin kwakwalwa wanda ke haddasa farfadiya daukewar ji ko ganin marar lafiyar
A wasu lokutan ma ayi asarar rayuwa baki daya.

A halin yanzu babu takamaiman maganain cutar kyanda, yin riga kafinta shine babban mahimmin abu sannan kuma idan an kamu da ita akwai hanyoyin da ake bi wajen sassauta radadin cutar, kamar misali shan magunguna da zasu saukar wa da mutum zafin jiki ko radadin jiki, Samun isashshen hut, Shan isasshen ruwa.


Kyanda cuta ce da ke yawo a Cikin iska ma’ana cutace da ake Dauka ta hanyar shakar iska ko amfani da wani abu da mai cutar ya taba.

Cutar kyanda na samuwa ne sanadiyyar wata kwayar VIRUS da ake kira MORBILLIVIRUS. Cutar tafi kama Kananan yara A duk lokacin da Aƙalla yara goma suke zaune guri guda tare kuma da wanda ke dauke da cutar, To akwai yiwuwar suma za su iya Kamuwa in har ba’a yi musu rigakafin cutar ba.

 

Suwaiba Abdullahi Sarki

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos