Home » Cutar Cancer Bakin Mahaifa

Cutar kansar bakin mahifa wato cervical cancer tana daya daga cikin cututtukan kansa da take kama bakin mahaifar mace, wato ta hanyar da da ke fitowa daga mahaifar ta, Kansar bakin mahaifa itace cutar daji ta hudu mafi shahara dake kama mata.


Hukumar lafiya ta duniya wato WHO tace a kashi 99 cikin 100 na matan dake kamuwa da kansar bakin mahaifa na da kwayar cutar Human Papilloma virus wanda kwayar cuta ce da ake saurin dauka ta hanyar saduwa.


Duk da cewa sau da yawa kwayar cutar kan mutu da kanta kuma ba lallai ta jawo wasu alamomi ba a jiki, idan ta dade a jikin mace ta kan haifar da kansar bakin mahifa.


Majalisar dinkin duniya ta yi kiyasin cewa a shekarar da ta gabata akalla mata dubu 604,237 aka tabbatar da sun kamu da cutar kansar bakin mahaifa a duniya.

Alamomin cutar sun hada da Ganin jini a lokacin da bana al’ada ba, Ciwon baya, kafa da mara, Matsalar fitsari da bayan gida, Jin zafi a lokacin saduwa.

Ana su da zarar mace ta fara saduwa da namiji ya kamata ta ringa zuwa asibiti ana yi mata gwaji a kai a kai, ta hanyar gwajin nan ne za a gano ko tana dauke da cutar a jikin ta.

Hanyoyin kariya daga cutar kansar bakin mahaifa sune
Yin allurar Rigakafin kwayar cutar, Gwajin bakin mahaifa

Cutar kansar bakin mahaifa nada saurin warkewa idan har an gano ta da wuri. Wato idan ba a bari tayi yawa ba, shiyasa Masana kiwon lafiya ke shawartar al’umma a kalla duk bayan shekara 3 zuwa 5 da su ringa zuwa asibiti a sake yi musu gwajin.

Da fatan za a dinga tuntubar likitoci kwararru akan matsalolin da suka shafi lafiyar gaba daya.

Nura Umar

View all posts

Add comment

Leave a Reply