Home » Taaddaci Na Cigaba Da Maida Cibiyoyin Kiwon Lafiya Baya

Najeriya, na ci gaba da kokawa dangane da yadda ayyukan ‘yan bindiga suka sa cibiyoyin kula da lafiya a yankunansu suka koma tamkar kufai sakamakon janyewar ma’aikatan lafiya.

Wasu daga cikin mazauna yankunan sun ce tuni wasu suka shiga aikin sa-kai na cibiyoyin lafiyar domin duba marassa lafiya, yayin da wasu suka kafa ƙungiyoyi don ganin sun samar da magunguna a asibitocin garuruwan nasu.

Mazauna yankunan da suke da wannan matsalar sun ce babban abin da ke damunsu shi ne duk wani jami’in lafiya da za a turo shi garuruwansu ba sa zuwa.

Sun ce saboda yadda ‘yan bindigar ke dauke jami’an lafiyar shi ya sa bas a zuwa ko da an tura su garuruwan.

Mazauna yankunan sun ce a wasu lokutan idan mace za ta haihu sai an yi tafiya mai nisa da ita kafin a samu asibitin za a kula da ita.

Kusan cibiyoyin lafiya 500 ne hukumar kula da lafiya a matakin farko a jihar Zamfarar ta ce ba sa aiki saboda matsalolin tsaro.

Dubban mutane ne ayyukan ‘yan bindiga ya tilastawa barin garuruwansu a wurare daban-daban na jihar Zamfara sakamakon yadda ake dauke mutane don neman kudin fansa.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro.

Suwaiba Abdullahi Sarki

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos