Home » Dajin Bakin Mahaifa

Kansa/Dajin Bakin Mahaifa wani nau`i ne na Daji dake shafar bakin mahaifar mace wanda ke kusa da gaban mace.

A lokacin da kwayoyin cuta ke kokarin shiga jikin mace, jikin na samar da nau`i na  kariya. Wannan kwayoyin halitta na kariya ne ke yawaita kuma su fara girma a matsayin dajin bakin mahaifa.

Hanyoyin da za`a bi don kare hadarin kamuwa da wannan cuta sun hada da gwajin cutar Dajin bakin mahaifar. Akwai kuma karban rigakafin cututtukan da ake dauka ta hanyar jimai.

A lokacin da mutum ya kamu da dajin bakin mahaifa, farkon abin da akeyi shine ayi aiki a cire dajin. Haka zalika ana karawa da shan magungunan kashe kwayoyin halittar da ke janyo dajin.

Sannan wannan cuta ta dajin bakin mahaifa, bata nuna alamomi a bayyane a lokacin da mutum ya kamu da ita.

Kara girman cutar kan sa ta bayyana alamomi kamar zubar jini a gaban mace bayan saduwa. Sauran alamomin sun hada da zubar da jini a lokutan da bata alada ko lokacin tsufa.

Zubar jini fiye da yadda mace ta saba, ko wuce kwanakin alada na daga allamomin wannan cutar. Zubar ruwa fiye da kima  ko fitar Ruwan mai karni a gaban mace, suma wasu alamomine na cutar.

Ciwon mara da kuma jin zafi yayin saduwa alamomi ne na wannan cutar Kansa/dajin bakin mahaifa.

Hanyoyin kariya daga wannan cuta ta Kansa/dajin bakin mahaifa sun hada da gujewa shan taba. sannan a kare kai daga jimai barkatai, yin gwaji a kai akai.

Bincike ya bayyana cewar za`a iya fara gwajin wannan cuta ta dajin bakin mahaifa daga shekara 21. kuma ana maimaita shi bayan wasu shekaru, da kuma tuntubar likitoci dacewar karban rigakafin wannan cuta.

Ana shawartar mata su guji anfani da sabulu ko wasu abubuwan daban a gaban su ko shan magungunan sanyi barkatai.

 

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos