MUN KUDIRI ANIYAR MAGANIN SHAYE-SHAYE TA HANYAR WASANNIN GARGAJIYA – ADAMU INUWA IBRAHIM.
Daga: Aisha Rabiu Musa
A cigaba da kawo karshen matsalar yawaitar shaye shaye dama masu lalurar tabin kwakwalwa a fadin kasar nan, a jahar Gombe kwamishinan matasa da wasnni na jahar Adamu Inuwa Ibrahim, ya bayyana cewar sun kudiri aniyar kawar da wannan matsala ta hanyar farfado da wasannin gargajiya a tsakanin matasan, Ire iren wadanda aka manta dasu tun a baya, Kamar langa, dambe, tsere, harma dai da kwallon kafa da dai sauran su.
Adamu yace hakan kan sanya su kauracewa shaye shayen da suke yi, Wanda harma takan kai ga illolin nata kan jefa wassu cikin wani mawuyacin hali na rashin lafiya, har takai wasu ma ga halaka rayuwar su baki daya.
Ya kuma kara da cewa, a yanzu haka sun hada Kai da ma’aikatar ilimi ta jahar, wajan taimaka musu a cikin wannan kudiri nasu da suke kokarin fara aiwatarwa, a cikin wannan sabuwar shekarar da muke tunkarowa.
To Sai dai wadannan wasanni yace bawai iya matasan zasu horar ba, harma da kananan yara da karfin su yakai suyi, Kamar yan ajin karshen na makarantun furaimari dana Sakandire wadanda za’a musu nasu horan a cikin makarantun su.
Kazalika Adamu Inuwa Ibrahim yace, hatta kasafin kudin shekarar 2024 da zamu shiga wanda aka gudanar dashi a gaban majalissa, an warewa wannan bangare nasu kasun, domin dai kawo karshen matsalar yawaitar shaye shaye da matasan keyi, ta hanyar sanya musu wasannin gargajiya da ka Iya rikesu a matsayin sana’ar da zasu dogara da ita, kuma su samawa kansu lafiya.
A karshe dai ya yabawa gwamnatin jahar ta gombe, ma’aikatar ilimi, dama duk al’ummar jahar tasu da suka basu gudummawa, wajan ganin tsarin nasu yakai ga gaci.
Add comment