Masana kimiyya sun ce za su iya yin gwajin da zai nuna yadda gaɓoɓi daban-daban na cikin jikin ɗan’adam ke tsufa, Hakan zai taimaka wajen hasashen gaɓar da za ta iya fuskantar matsala a gaba.
Wasu Tawagar masanan a Jami’ar Stanford sun ce za su iya sanya ido kan manyan gaɓoɓi 11 na jikin ɗan’adam, ciki har da zuciya da ƙwaƙwalwa da kuma huhu.
Masanan sun gwada yin haka a kan dubban mutane masu matsakaitan shekaru da kuma waɗanda suka fara tsufa.
Binciken ya gano cewa kowane mutum ɗaya a cikin mutum biyar masu lafiya, wadanda shekarunsu suka kama daga 50 zuwa sama, kan samu aƙalla gaɓa ɗaya a jikinsa da ke saurin tsufa fiye da saura.
Sannan kuma mutum ɗaya zuwa biyu cikin mutum 100 kan iya samun gaɓoɓi da dama a jikinsu da suka fi sauran jikinsu tsufa idan aka kwatanta da shekarunsu na haihuwa.
Duk da cewa yin irin wannan gwaji zai iya kasancewa mai ban-tsoro, amma wata dama ce ta yin rigakafi game da duk wata matsala da wata gaɓa za ta iya samu a shekaru masu zuwa, kamar yadda masanan suka faɗa.
Sanin gaɓar jiki da ke tsufa fiye da shekarun mutum zai taimaka wajen gano irin rashin lafiyar da mutum zai iya fama da ita a gaba, kamar yadda masanan suka faɗa a wata mujallar bayanai kan halittu.
Misali, zuciyar da ke tsufa fiye da shekarun mai ita za ta iya haifar da haɗarin samun ciwon zuciya a gaba, haka nan idan ƙwaƙwalwa na tsufa fiye da shekarun mutum hakan na iya alamta cewa mutum zai samu cutar mantuwa.
Binciken ya nuna cewa, idan mutum na da wata gaɓa ko gaɓoɓi da ke tsufa fiye da shekarunsa, to za a iya hasashen cutar da mutum zai fuskanta ko ma mutuwa a cikin shekaru 15 masu zuwa, dangane da ita gaɓar ko kuma gaɓoɓin.
Add comment