Home » Watan Ramadana

Wasu Shawarwarin da Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya wato WHO Ta Fitar dangane da azumtar watan Ramadana.

Kuma yana da muhimmanci mu bi su yayin azumtar wannan watan domin samun ingantacciyar lafiya.

Musulmi a Fadin Duniya baki daya suna azumtar azumin watan ramadana.

Wannan wata ne mai Albarka dake cike da abubuwa da dama. kuma wata ne na Ibada, watan Zaman Lafiya da Kaunar Juna a Tsakanin al`umma.

Lokacin azumi, mutane na yin Sahur da Asuba Kafin Ketowar Alfijir sannan a Sha Ruwa da Magariba ko faduwar rana Wato Iftar. Ya na da muhimmanci sosai al`umma su kula da yanayin abincin su.

Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta bada bayanai kan tsarin cin abincin da ya dace a lokacin azumi. Ana so Aci Abincin dake da dauke da dukkan Sinadarai masu anfani ajikin dan adam Hakan na da mahimmanci sosai. A guji yawan cin abincin da ke da maiko yayin buda baki. Mu tabbabtar da cewa mun sha Ishashshen Ruwa ko yayan Itatuwa masu ruwa sosai da kuma abincinda ke da Sinadarin gina jiki.

A rage yawan cin gishiri a lokacin azumi. Za`a iya maye gurbinsa da sinadaran gargajiya masu anfani a jikin `dan adam.

Motsa jiki shima wani muhimmin abune a wannan watan na ramadana. Yayin da aka ci aka koshi a na so a samu motsa jiki. wannan zai taimaka wa jiki ya  anfana da abincin da kuma kare lafiyar jikin.

Mu Kauracewa Shan Taba Sigari Ko Shisha da sauran kayan maye. Hakan zai taimaka wajen kare lafiyar zukatan mu da sauran sassan jiki baki daya.

Yawan cin soyayyen abinci kan zama illa ga lafiyar mu. Zamu iya canza yanayin girkin mu daga soyawa zuwa gashi ko turarawa domin samun anfanun da ya dace. Ganyayyaki da kuma kayan itatuwa na da matukar muhimmanci ga lafiyar mai azumi.

Allah ya bada ikon Azumtar ramadana cikin koshin lafiya.

 

 

Yabintu Abubakar

View all posts

2 comments

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos