Home » Wata Cuta Ta Barke A Daya Daga Cikin Jihohin Arewa

WATA CUTA TA BARKE A DAYA DAGA CIKIN JAHOHIN AREWACIN KASAR NAN.


Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta sanar da bullar cutar zazzabin Dengue a wasu kananan hukumomi uku na jihar Sokoto.

Zazzabin Dengue cuta ce da sauro ke haifar da ita wanda a mafi yawan lokuta aka fi samunta a wurare da suke da yanayi na zafi kuma tana yaduwa ta hanyar cizon dabbobi ko kuma kwari.

Mutanen da suka kamu da cutar dengue kan nuna wadansu kananan alamu, a wasu lokutan ma basa nuna wata alama ta cutar, haka kuma alamun yawanci suna bayyana tsakanin kwanaki 4-10 bayan kamuwa da cuta.

Wasu daga cikin alamun sun hada da zazzabi mai zafi, fesowar kanana-kananan kuraje da ciwon gabobi. Idan kuma cutar tayi tsanani takan haifar da zubar jini mai da jijjiga, wanda zai iya zama barazana ga rayuwa.

A wani rahoto da hukumar ta fitar ranar Lahadi, NCDC ta ce an gano zazzabin Dengue a jihar a watan Nuwamba.
Hukumar ta ce a halin yanzu jihar na da mutane 13 da aka tabbatar da sun kamu da cutar sannan kuma da wasu 71 da ake zargin suma sun kamu.

“Hukumar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) tana sane da barkewar cutar zazzabin Dengue da aka ruwaito a jihar Sokoto a watan Nuwamba 2023. Ya zuwa yanzu, mutane 71 ne ake zargi sun kamu da cutar, yayin da aka tabbatr da mutane 13 na dauke da cutar kuma babu mace-mace a jihar.” Kamar yadda sanarwar ta ayyana.

“A halin yanzu, an sami rahoton bullar cutar a kananan hukumomi uku (3) (LGAs): Sokoto ta Kudu (60), Wamako (3) da Dange Shuni (1). Yawancin wadanda ake zargi da kamuwa da cutar sun kasance tsakanin shekaru 21-40.

Hukumar ta ce kididdigar da aka gudanar game da barkewar cutar ya nuna cewa a halinzu cutar tana matsayi na saisa-saisa. Sa’annan ta kara da cewa jihar Sokoto ce kadai aka samu bullar cutar, kuma kawo yanzu babu rahotan mace-mace ta dalilin cutar, inda ta kara da cewa an dauki matakan da suka dace don dakile barkewar cutar.

Umar Abubakar Imam

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos