Home » WANKE GASHI

Wanke Gashi na cikin abubuwan da Mutane Suka damu dayi, Tsawon wani lokaci Yakamata a dauka kafin a wanke gashi? Kullum-Kullum KO bayan Wasu Kwanaki?

Masana sun bayyana cewar Akalla ana Bukatar wanke gashi sau daya a duk Sati. Amma ya danganta da yanayin gashin da kuma fatar kan mutum. Daga karshe dai, dole Mutum yayi la`akari da Yadda yafi kike gamsuwa da shi.

Sanin yaushe ya kamata a wanke gashi ya na ga maida hankali ga lafiyar gashin. Jin tsami ko kaikayi, na bada alamar lokacin wanki ya yi.

Sannan kuma wanke Kai ba kowanne irin wankewa ake nufi ba. Sanya sabulun wanke gashi ba tare da jika gashin ba kan tsananta kaikayin ko kuma ya haifar da Amosanin gashi. Idan kuma aka dau tsawon lokaci ana wanke shi, ya kan zamo silar shigan kwayoyin cuta ta Bakteria ko wani ciwon daban.

Gashin da ke da cika da kuma tauri baya daukan datti da wuri. Za`a iya daukan sati daya zuwa sama kafin a wanke shi. Ba kamar wanda bashi da cika mai laushi ba. Saboda yafi kama datti da wuri. Kuma ya kamata a wanke shi bayan kwana biyu.

Ga masu wadannan nau`in gashin kuma masu aikin wahala ko kuma zufa sosai. Zasu iya wanke shi kafin wadannan lokutan da aka  bayyana. Wannan ba wata doka bace bisa ga bincike. Haka zalika, Mutum zai iya lura da gane wanne gashin yafi bukata. Cikin la`akari da gujewa yawan wanke shi da kuma barin shi da datti.

Shawara kan yadda za`a wanke gashi. Kada ayi hanzari, a fara da jika gashi na dan wani lokaci, kafin a Sanya sabulun wanke gashi (Shampoo). Idan aka jika shi dattin zai fi sauka da wuri.

A Sanya sabulun a kasan gashin ba a bakin gashin ba. Sanya shi a bakin gashin kan Sanya karyewan gashi. Musamman ma idan gashin a bushe yake. A lokacin da za`ayi anfani da man Kondishina (Conditioner) a Sanya shi daga baki-baki.

A rage yawan anfani da mayika masu karfi ko turaren gashi da yawa. A wasu lokutan, su kan sanya cushewar datti a gashi su hana shi girma da kuma Sanya shi bushewa.

Wanke shi a dai-dai lokacin da ya kamata kan rage taruwan wadannan mayikan da kuma bada dama asalin danshin gashi ya samu fitowa. wannan zai inganta Lafiyar Gashi.

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos