Home » Tsadar Magunguna Ya Sanya Al’umma Da Dama Zama Da Cututtuka A Jikinsu

TSADAR MAGUNGUNA YA SANYA AL’UMMA DA DAMA NA ZAMA DA CUTUTTUKA A JIKIN SU.


An bayyana Najeriya a matsayin kasar da tafi hadahadar magunguna fiye da kaso 70 na magungunan da ake shigowa dasu daga kasashen indiya, China, dama dai sauran kasashen ketare.

Baya ga haka, wasu nau’ikan magungunan akan neme su ne a rasa a shagunan masu siyarwa da asibitoci, ta yadda Sai mara lafiya ya yi tafiya zuwa wasu gurare masu nisa kuma a farashi mai tsada kafin ya samu, sabanin yadda ake siyar dashi a baya.

Wanda hakan ke neman gagarar kundila a yanzu, Musamman ga marasa lafiyar da cututtukan nasu suka fi tsamari, Kamar dai masu dauke da cutar kansa, zuciya, hunhu dama ciwon hanta, inda wasun su suka koma nema maganin jifa-jifa ba Kamar yadda yake a likitance ba.

Shugaban Kungiyar masu hada magungunan na kasa, Farfesa Cyril Usifi ya dora laifin tashin farashin ga sinadaran hada magungunan masu karfi (APLs).
Sannan yace abubuwan da muke amfani dasu ba’a kasar nan ake siyo su ba, kuma ya danganta ga farashin da muka siya, baya ga hakan babu wutar lantarkin da zata sarrafa sinadaran.

A bangaran wani magidanci da ya bayyana mana yadda tashin magungunan ke neman jefashi cikin wani yanayi na damuwa, yace a da duk wata yakan kashewa mahaifiyar sa dubu 10 zuwa 12, amma a yanzu haka yakan kashe fiye da dubu 20, kuma hakan na fin karfin samunsa.

Shima wani mai saida magunguna ya bayyana mana rashin Jin dadin su kan tsadar Magunguna, ta yadda masu siyan kan kasa a wani lokacin Sai dai su zauna da cutar a jikin su ko kuma su nemi mai saukin da zai rage musu radadin ciwon, wasu kuwa tuni suka koma shan magungunan gargajiya.

 

 

 

Umar Abubakar Imam

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos