Home » Shawara ga Iyayen Yara

Iyayen Yara na da Muhimmiyar Rawa da suke takawa a rayuwar `ya`yan su.

Masana halaiyyar yara sun gudanar da bincike kan muhimman hanyoyin da iyayen yara za su bi domin girmar da yayan su cikin kulawa da kuma cikakkiyar lafiya.

Da farko dai, ko wani Uba ko Uwa ya kamata su tabbatar cewa anyi wa yayan su rigakafin cututtuka. Musamman kan cutukan da ke halaka yara kanana a lokacin yarinta. Rigakafi shine hanya ta farko da iyaye zasu tabbatar da lafiyar yayan su tun daga haihuwa har zuwa shekaru goma sha shida.

 

rigakafi
rigakafi

Rigakafin kan Basu Kariya daga Kamuwa da cututtuka kamar su farankama, ciwon hanta, muran mashako, shan inna, kyanda, sankarau, da sauransu. Idan iyaye suka baiwa yayan su kariya ta wannan hanhar tabbas shine gata mafi girma a garesu.

Na biyu shine ware wa yara wajen kwanciya. Yawancin iyaye na ganin kwantar da yayan su kan gadajen su ko simfidunsu, su kwana tare shine gata.

Amma bincike ya nuna cewar yawancin iyaye dake kwanciya da yayan su kan Sanya `ya`yan su shiga wasu yanayi kamar na danne musu hanci yayin juyi ko shayarwa. Hakan ke sa a samu yaro ya rasa nunfashi, suma ko ma mutuwa baki daya. Harwa yau sun kara da cewa kula da yanayin kwanciyar yaro na da mutukar anfani. Yaran dake kwanciya gefe ko ta baya a lokacin da suke bacci sun fi wadanda ke kwanciya ruf da ciki lafiya. Sun kuma shawarci iyaye da su samar wa yayan su makwanci daban da nasu, sannan su kula da yanayin baccin su.

Abu na gaba shine, samar wa yara kanana kujerun zama a mota, wannan na nufin kujerun da ake anfani da su ga yara a mota lokacin da iyayen su ke tuki. Sannan a tabbatar da yara da suka dan taso, na anfani da madauri na kujerun mota (seat belt).

kujerar moto
kujerar moto

A tabbatr da cewa yara na zama a kujeran baya a mota domin kare su daga jin mummunan Rauni a lokacin da mota ta samu hadari. Haka zalika  zasu kare iyayen daga hadari ta hanyar dauke hankulan su daga tukin.

Kula da yara a wurare da ke da rafi ko rijiya, ko kuma wajen iwo da wanka a ruwa. Koda kuwa na cikin gida ne. Masana sun binciko cewa da yawan yara na fada wa ruwa kuma wani sain ma a rasa su. Don haka yana da muhimmanci a kula a duk lokacin da suke kusa da ruwa. Sau tari akan samu wasu iyayen da sakaci na barin manyan mazubin ruwan anfanin gida a bude. Wannan kan ja raayin yara su kama wasa da su, har ma ta kai ga illa a rayuwar su.

wasan ruwa
wasan ruwa

A wani lokacin wasan yara a ruwa kan kai su ga samun cuta da suke yaduwa ta hanyar ruwa. Cututtuka kamar fitsarin jini, tsusan ciki, da wasu cutukan fata.

A matsayin mu na iyaye, ya Kamata mu kula da rayuwar `ya`yan mu. Mu bi tsarin shawara ga iyayen yara domin su tashi cikin koshin lafiya da walwala.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos