Home » RUWA ABOKIN RAYUWA

Ruwa Abokin Rayuwa. Kamar Yadda Kowa Ya Sani Ruwa abu ne da ake Bukatar a mai da Hankali kansa. Ruwa na da Muhimmanci a Rayuwar Kowa da Kowa Musamman Yara Kanana. Bincike ya nuna Cewa Mutum Zai iya Zama Tsawon Mako Uku ba tare da yaci Abinci ba Kuma Ya Rayu Babu Wata Matsala. Amma abin ya sha ban-ban a Bangaren Ruwa. Ruwa shine Abokin rayuwar Kowane Dan Adam.

Muhimmancin Ruwa ga Yara. Yara na Saurin Kone Ruwan dake Jikin su Fiye da Manya. Hakan na da Nasaba da yawan tsalle-tsalle da suke yi, wasa da sauransu. Saboda rashin kwarin jiki, suna saurin samun yanayi na zazzabi, Amai ko Gudawa da kan Sanya Ruwan jiki karewa da sauri.

Ba sai yaro ya nemi ruwa Ba Yakamata a bashi. Wani lokacin ko da bai nema ba, Jikin sa na bukata. A wannan yanayi ya dace a basu ruwa akai-akai saboda Muhimmancin Ruwa a Rayuwarsu musamman idan basu da lafiya.

Wasu daga cikin Manyan Dalilai da ke Nuna Muhimmancin Baiwa Yaro Ruwa Sun Hada da;

Shan Wadataccen Ruwa na Sanya Jiki Gudanar da Aikinsa yadda ya Dace. Bincike ya bayyana Cewa Kaso 75% na Yara ba sa Samun Su Sha Wadataccen Ruwa da Jikin su ke bukata. Karancin Ruwan kan Sanya yaro yawan Gajiya, Ciwon Kai da kuma Karancin Anfani Abinci a Jikin Sa.

Ana Bukatar a Ajiye Ruwa a kusa a koda Yaushe, ko da  a mota ne domin kishin ruwa na yara ba kamar na manya bane. A basu Ruwan akai-akai musamman idan suka dawo daga makaranta a gajiye. A basu ruwa mara sanyi, saboda mai sanyin kan haifar musu da ciwon kai a lokacin da suke da gajiya.

Na biyu Ruwa na Taimakawa Yara Masu Ciwon Sarkewar Numfashi Wato (Asma). Yara na Bukatar Ruwa Sosai Musamman Lokacin da Suke Girma. Rashin Samun Wannan ka iya Haifar Musu da Ciwon Tari na Asma. Lokacin da akaga Yara suna tari sosai a dan basu ruwa kadan a kuma lasa musu Gishiri kadan a harshe zai taimaka wajen Tsayar da Tarin.

Shan Ishashshen Ruwa na kare Yara Daga Jin Yunwar Dare. Wani lokaci yaro zai tashi cikin dare da yunwa. Amma idan aka bincika, zaa ga ruwa yake tsananin bukata wanda har yake ji kamar yunwa ce. Shan ruwa awa daya ko minti talatin kafin a kwanta zai taimaka da rage wannan. Wani lokacin wannan ba zai sa su yawan fisari ba idan har jikin na bukatar Ruwan.

Rage Gajiya da sa Yaro Saurin Fahimta. Shan ruwa na kara kuzari, mai da hankali, da nutsuwa ga yaro. Rashin ruwa kan sa yaro gajiya da rashin nutsuwa. Yaron da ya sha ruwa ishashshe ya fi maida hankali ga abin da ake koyar da shi. Yana kuma kara lafiyar kwakwalwar yara. Shan ruwa yana hana yara Ciwon Jiki da Gabobi. Yara na samun ciwo a lokacin da suke girma. Shan Ruwan na taimaka musu da kare su daga wannan ciwon. haka Kuma zai Taimaka wajen Rage hadarin kamuwa da Ciwon Daji. Yara kananan da ke shan ishashhsen ruwa, basa cikin hadarin kamuwa da ciown daji na jini da ma sauran sassan jiki.

Wannan Shan Ruwan ba shi da hadi da lemon kwalba ko na roba. Saboda wadannan nada hadari ga lafiyar yara. Iyaye na ganin cewa ai yaron ya sha lemu a wani sa`in. Zaki ko suga dake cikin wadannan lemukan kan Sanya yaro jin kishin ruwa da kuma haifar musu da wasu matsalolin daban.

Lokacin da yara suka soma tasowa. Shan ruwa na taimakawa wajen inganta lafiyar fatar jikin su. Kare su daga Kuraje, Kaikayi, Bushewa, Laushi da Kuma Sheki.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos