Home ยป Rage Damuwa A Lokacin Gajiya

Akwai Wasu Muhimman Hanyoyi guda shida da zamu Iya bi wajen rage damuwa. Wadannan Hanyoyin zasu taimaka wajen inganta lafiyar mu da kuma fidda gajiya a Tare damu.

Rage Damuwa yayin gajiya abune mafi muhimmanci ga rayuwar mu. Gajiya wata aba ce da ta zamo tilas cikin rayuwar yau da kullum. Saboda haka, ya zama tilas mu kula da yadda zamu rage damuwa a lokacin da gajiya ta zo mana.

Hanyar lura da nunfashi; wannan hanyar na nufin jan dogon nunfashi tare da kirga daga daya zuwa biyar, sannan a rike nunfashin a sake kirga biyar, kafin nan a sake a hankali ana kirgen daga daya zuwa biyar. A maimaita hakan har na tsawon mintuna uku zuwa biyar. Wannan na daga cikin hanyoyin mafi sauki da baa bukatar taimako.

A lokacin da mutum yayi wannan yadda ya dace, zai ga cewar gajiyar na sauka a hankali. haka zalika wannan ma na taimakawa masu ciwon hawan jini.

Na biyu shine Samun hutu daga anfani da wayar hannu; Mafiya yawan mutane na bada muhimmanci sosai wajen wasa da waya ko kuma anfani da Ita sosai. Wannan na daukar mafi yawan lokacin su. Idan aka dauki hutu na wani lokaci daga anfani da wayan zai taimaka wajen rage damuwa da gajiya.

Yin nazarin muhimman abubuwa; Masana sun bayyana cewar a lokacin da mutum ya samu Gajiya da kuma shiga damuwa. Yana da muhimmanci ya koma nazarin irin abubuwan da ke kwantar masa da hankali. Wannan zai taimaka wajen samun nutsuwa da kuma kwanciyar hankali.

Abu na gaba shine shan shayi mai zafi; Lokacin da mutum ya kasance cikin damuwa, shan kofin shayi mai zafi cikin nutsuwa zai taimaka. A wannan lokacin ba shan shayin kadai ba, mai da hankali kan dukkan abin da shayin ya kunsa na da muhimmanci. Kamar dandanon shayin, zafin shi, yanayin kofin da sauransu. Wannan na da matukar anfani musamman a wuraren aiki. Zaka samu yan mintuna da zai kawar da tunanain ka daga abin da ya saka ka gajiya da kuma damuwa.

A samu shan iska na yan mintuna; fita daga wuri ko yanayi da ya Sanya gajiyan na yan mintuna zai taimaka. Ko a samu a dan zaga ko kuma a dan tsaya daga gefe don shan iska. Wannan zai iya kasancewa wani sa`in a bakin ruwa, ko Kallon sararin samaniya da sauran halittu.

Na karshe shine samun nishadi; mutum ya samu lokaci da masoya ya dan yi hira, wasa da kuma Dariya. Babban hanya da zai sa mutum ya manta da damuwar da yake ciki shine samun lokaci da masoya. Dukkan gabobin jiki na samun nutsuwa a wannan lokaci.

Yabintu Abubakar

View all posts

2 comments

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos