Home » Nonon Mace (Breast)

Nonon Mace (Breast) Na Bukatar Matukar Kulawa. Nono na Daya Daga Cikin Muhimman Abubuwan da ya dace Mace Take Tinkaho Da Su. Musamman Sabada Daga Daraja da Kuma a Wajen Mai Gida dama Ita Kanta.

Akwai Abubuwa da Dama da Mace ke Fuskanta a Lokacin da Shekarunta Suka Ja. Daga Ciki akwai Zubewar Nono. Akwai Bukatar Mace ta San Hanyoyin da zata Wajen Kula  dasu.

Bincike ya Nuna Cewar Abubuwa da Dama na Sanya Zubewar Nonon Mace. Wadanda Suka Hada da Shekaru, Kiba, Shan Taba, Motsa Jiki ba Tare da Amfani da abin da zai rike su ba. Yanayin Siffar Jiki, Yawan Tsalle-Tsalle, Juna Biyu, Shayarwa da Sanya Rigar Nono wadda Batayi Dai-Dai dasu ba. Sannan da Yawan Amfani da abinda zai Danne su Kamar Daurin ‘Kirji ko Riguna Masu Tsayawa kan Nonon da Sauransu.

Koda Yake Rigakafi Yafi Magani. Matakan Kariya Daga Zubewar Nonon Mace (Breast) Suna Farawa ne Tun Mace tana Budurwa ko Lokacin da ta Fara Kirgen Dangi. Akwai Matakan Da Mace Zata Iya bi Wajen Tattalin Nonon ta da Kuma Kare Shi Daga Zubewa. Wadannan Hanyoyin Kamar Yadda Masana Suka Bayyana sun Hada da;

 • Rage Yawan Jijjigasu; Rage Tsalle-Tsalle ko kuma Amfani da Rigar Nono (Bra) da zai Rike Nonon ya Hana Su Yawan Jijjigasu Yayin Motsa Jiki. A Lokacin da ba na Motsa Jiki ba, Yakamata Mace ta yi Amfani da Rigar Nono Dai-Dai da Nononta Domin Gujewa Matse su ko Yawan Sakinsu.
 • Kiba, Madaidaicin Jiki Zai Taimaka Wajen Kare Mace Daga Zubewar Nono.
 • Shan Taba ko Giya; Shan Kayan Maye na Kashe Kwayoyin Halittar Jiki. Yana kara Tsufa Sosai, Don Haka zai Sanya Kwayoyin Halittar Nonon su Mutu da Wuri Kuma Nonon ya Zube.
 • Abinci; Jikin Mace a Kowanne Lokaci Yana Bukatar Ingantattun Sinadarai Domin Kara Lafiya, Kyau da Kuma Kuzari. Cin Abinci Mai Kyau Nada Matukar Amfani ga Nonon Mace zai Taimaka mata Wajen Hana Zubewar Nonon Tun Tana Budurwa. Dukkan Abincin da Mace Zata Ci Domin Gyara Nonon Zai Taimaka Wajen Hana Zubewar Nonon Tun Daga Farko.

Akwai wasu Hanyoyi da Masana Kiwon Lafiya Suka Bayyana Wajen Gyaran Nonon Mace. Wadannan Hanyoyin sune;

 • Abici; Cin Abinci Da Ka Iya Taimakawa Wajen Hana Zubewar Nono da Kuma Kara Lafiya Irin su Lentils, Madara, Kifi Mai Maiko, Kwai, Wake, Kurkum, Plums, ‘Ya’Yan Kabewa, Sanflawa, Flax Seeds, Sturoberi, Tanjirin, Ganyayyaki Kamar su Kabeji, Kolifawa, Brokali. Tsabar Chia, Dangin Gyada. Kunun Aya, Alkama, Hulba da Dabino. Haka Zalika Garin Zogale.
 • Tausa; Amfani da Man Hulba ko Zaitun Mai Dumi Wajen Shafasu a Nonon Ana ‘Dagasu Sama yana Taimakawa Wajen Musanya Matattun Kwayoyin Halittar Nonon da suka sanya su Zubewa.
 • Shafa Kankana na Tsawon Mintuna Biyu a Kullum na da Alfanu Wajen Gyaran Nono.
 • Garin Hulba; Ana Dama Garin Hulba da Ruwa yayi ‘Dan Kauri Sannan a Shafa shi a Nonon na Tsawon Mintuna 10 Zuwa 12 Sannan a Wanke shi.
 • Danyan Kwanduwar Kwai da Gurji; Ana Hada Markadadden Gurji da Danyan Kwanduwar Kwai a Shafa akan Nonon ana Daga shi. Sannan a wanke Bayan Mintuna 30.
 • Alobera; Ana Shafa Markadadden Alobera a Jikin Nonon Sannan a Wanke Bayan Mintuna 15.
 • Motsa Jiki; akwai Nau`ukan Motsa Jiki da dama da akeyi domin Tsayar da Nono. Akwai wanda ake kira da “Push Up, Plank, Twist” da sauran su.
 • Ana iya Gudanar da Aiki (Tiyata) Domin Rage Girman Nono da kuma Cire Fatar da Tayi Yawa domin Tsayar da shi a Asibiti.

Kwanciyar Hankali na daga Cikin Manyan Ababen Dake Taka Rawa ga Lafiyar Jikin Mace. Hakama Gyaran Nonon ba`a bar shi a baya ba. Ba abin Kunya Bane Idan Nonon Mace ya Zube, sai dai yana da matukar Amfani a Gyarasu Domin Kasancewa abin sha`awa Wajen Mai Gida.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos