MUHIMMANCIN KULA DA LAFIYA DA WALWALAR DABBOBI
Kamar yadda lafiyar mutane take itama lafiyar dabbobi tana da mahimmanci kuma tana da sarkakiya da kalubale kunshe cikinta.
Cigaban fasahar zamani, Kere Kere, da Kuma Hanyoyin Samar da magunguna, binciken kimiya Duk Sun Samar da mafita ga cututtukan dabbobi.
Hakan kuwa ya shafi manyan da Kananan dabbobi na gida da na Dawa, halitun ruwa da sauransu. lafiyar dabbobi abace Mai mahimmanci kwarai da gaske.
Ma,aikatan lafiyar dabbobi da likitocin Sune masu daukar gabaran tabbatar da yanayi na zahiri ga lafiyar dabbobi da walwalarsu. Kuma Suna taimakawa wajan bawa dabbobi kariya, da warkar dasu daga cuttukan da suke damunsu.
Dan Adam Yana mu,amala da Dabbobi a kullum a rayuwar sa. Wannan Dabbobin sun hada da Dabbobi gida dana daji. Lafiyar su da walwalarsu tana da mutukar anfani, domin samun lafiyar Al,umma, da samun wadatacan abinci, Cigaban Tattalin Arziki da Kuma Kare Muhalli.
An fayyace cewa kusan duk cuttukan da suka shafi Al’uma sunsamo asali daga dabbobi, kamar irin su HIV, EBOLA da sauransu. Kuma wannan na faruwa Sakamakon sauyin yanayi da yake taka muhimmiyar rawa wajan yaduwarsu.
Kaso 60 na kwayoyin dasuke haifarwa Dan Adam cututtuka sun samo asali ne daga jikin dabbobi gida Dana daji.
Lafiyar dabbobi da walwalarsu wajibine domin dabbobi suna samarwa Dan Adam wata garkuwa wajan samarmasa da abinyi da Kuma tabbatar da wadataccan abinci.
Baduk cutar dabbobi ce ke da tasiri Kai tsaye ga lafiyar Al,uma ba. Cututtukan dake addabar Dabbobi sukan shafi zaman takewa da tattalin arziki mu kaitsaye.
Rashin lafiyar dabbobi ba Cutace da zata taba lafiyar Al’uma kai tsaye ba saidai tana iya taba hanyar samarwa da Al,uma aikinyi.
Mutum 1 Cikin mutune 5 ya ta,allaka da Dabbobi wajan samun kudin Da zai dauki dawainiyar rayuwar sa gaba daya.
Haka Kuma sama da Kaso 70% na abincin da ake samu daga Dabbobi ne. Wadannan Nauikan Abincin Sune madara, nama kwai da dai sauransu.
Karuwar Chanjin yanayi Yana zuwa da kalubale ga dabbobi, don haka Kula Da walwalarsu ya taallaka ga sabbin tsare tsare kamar bukatar a Gina wadatun kayan kula da Dabbobi, irin su asibitoci dakunan gwaje gwaje, bincike da Samar musu da abinci Mai inganci da zai gina musu jiki.
Kaso 66% na halittin ruwa dana kan tudu irin su tsirrai sunsamu nakasu ga walwalarsu sakamakon sauyin yanayi a dalilin abubuwan da Al,uma keyi.
Mu sani cewa bawai samarwa da Dabbobi ingantacciyar Lafiya kawai shi ne muhimmin abun lura ba, hatta kula da walawalar su shi ma abun lura ne, domin kuwa walawalar Dabbobi walawalar al’umma ce.
Add comment