Home ยป Mace Mai Shayarwa

Muhimman Abubuwa da ya Kamata Mu Sani Dangane da Shan Magunguna ga Mace Mai Shayarwa.

Ya na da Muhimmanci Mace Mai Shayarwa ta Guji Shan Magani idan ba ya zama Tilas ba.

Wajibi ne Mace Ta Shayar Da Jaririnta Nono Sosai Kafin Ta Sha Magani Idan Akwai Bukatar Hakan. Kasancewar Manganin zai dan bi Jikin ta. A tabbatar an sanar da Likita Batun Shayarwar Kafin ya bada Magani ga ita Mahaifiyar.

Akwai wasu magungunan da ke sanya yaron da ake Shayarwar ya samu wasu Matsalolin Kamar su Gudawa, Yawan Bacci, Dama Canji a Jikin sa da Suka Hada Da Yawan Kuka ko Rashin Nutsuwa.

Wasu Magungunan da Basu da Matsala ga mai Shayarwa sun Hada da, Duk Wani Magani da ba Zai sa Uwar Tayi Bacci ba. Ko Maganin Digawa a Ido ko Kunne, da na Shafawa a Jiki.

Duk Wani Magani da zai saka ita Mahaifiyar Bacci zai Saka Shima Abunda Take Shayarwa Bacci Kuma zai iya zame masu illa ta wajen rashin samun Ishashshen Abinci.

Magungunan da ake kira da Antibayotik na yakar Cututtukan da Kwayoyin Cuta ke Haifarwa. Amma yana da Muhimmanci a Tuntubi Likita kafin ayi Anfani da su. Haka zalika wasun su na sanya Ruwan Nono ya yi Daci wanda Hakan Yake sa Jarirai basa son shan Nonon.

A lokacin da Uwa ke Fama da Mura, yana da muhimmanci tayi anfani da maganin shaka a hanci. Kada ta sha maganin da ke dauke da sinadarin Pseudoephedrine a cikinsa. Sannan ta tuntubi likita domin shawara kan maganin da ya dace ta sha idan mura Tayi Tsanani.

A kiyaye shan Magungunan Ciwon Jiki Kamar su Ibofrofen da Makamantan su. Magungunan masu karfi na da matsala ga abin da ake shayarwa.

Mai Shayarwa da Take da Bukatar Daukar Rigakafi Saboda Wani Dalili na Bukatar Tabbacin Rashin Matsalar Wannan Rigakafin Daga Wajen Likita.

Dukkan Uwa dake shayar wa kuma take shan magani ta kula da Yanayin Bayan Gidan Yaronta, Baccin sa da kuma cin Abincin abin da Take Shayarwa.

Wasu yanayin kan Sanya a tilasta Uwa dakatar da shayarwa saboda wani magani da take sha bisa larura.

Kamar Magungunan Asibiti, Shima Maganin Gargajiya na Daukar Wannan Yanayi. Su Kan Zamo Illa Sosai ga mai Shsayarwan da ma Kari Kan na Asibiti. Saboda yanayin sa na rashin Takamamman Adadin da ake Sha, Zai iya Kasancewa yafi Kafin Dan da ake Shayarwa.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos