Home » Lemun Tsami (Lemons)

Lemun Tsami (Lemons) na cikin abubuwa masu matukar anfani ga lafiyar al`umma. Yana daga `ya`yan itatuwa masu kunshe da tarin Bitamin C a cikin sa. Lemun Tsami na Cikin ababen da ke rage Hadarin Kamuwa da Matsalolin Zuciya da Ciwon Daji. Sannan kuma yana da sinadaran da ke da anfani wajen rage ‘Kiba da kuma inganta Lafiyar Jiki.

Bisaga tarin sinadaran da ke cikin Lemun Tsami (Lemons), yana da dumbin alfanu ga jiki da lafiyar dan adam.

Inganta Lafiyar Jiki: Sinadaran Bitamin C da kuma Folet dake cikin Lemun Tsami na Inganta Lafiyar Jikin Dan Adam da kuma ‘Karfafa Kwayoyin Halittar Mutum. Wannan zai taimaka wajen kare mutum daga cututtuka da kuma rage damuwa.

Shanyewar Barin Jiki: Sinadaran dake cikin wannan `ya`yan itaciya na hana Daskarewar Jini a cikin jiki. Wannan kan kawar da hadarin kamuwa da Shanyewar Barin Jiki Sakamakon Toshewar Hanyar Jini.

Hawan Jini: Sinadarin Flebonoid dake cikin lemun na rage Hawan Jini. Ruwan lemun nada anfani wajen gudanar Jini a Jiki. Sannan ya kawar da Hadarin Kamuwa da Cutar.

Ciwon Daji: Bincike ya nuna cewar masu anfani da lemun Tsami na bada Kariya daga kamuwa da Ciwon Daji da kaso 20 fiye da wanda basu anfani da shi. Haka kuma sinadaran dake kunshe cikin bawon lemun na da yanayi na kariya daga Ciwon Daji musamman ma na Hunhu.

Tsufa: Bincike ya nuna cewar sinadaran da ke cikin lemu na kawar da Lalacewar Kwayoyin Halitta, Yankwanewar Fata, da kuma Kaurinta. Wannan ke Sanya Rashin Tsufa ga mutane da kuma samun Ingantacciyar Lafiyar Fata.

Cutar Sarkewar Nunfashi: Bincike ya nuna cewar anfani da lemun tsami, `ya`yan itatuwa da Ganyayyaki na da Tasiri Wajen Rage Hadarin Kamuwa da ciwon sarkewar nunfashi.

Anfani da lemun tsami na Taimakawa Jiki wajen Tatsar Sinadarin Ayon cikin abinci. Hada abincin dake dauke da Sinadarin Ayon da kuma Lemu na Sanya Samun wadataccen Ayon a jiki. Hakan na samuwa ne saboda yanayin sa na Sanya Tatsar Ayon din.

Rage Kiba: Anfani da wannan `ya`yan itaciya na Sanya Saurin Koshi. Sinadaran dake cikin sa na Sanya Mutum Koshi da kuma rage yawan cin abinci. Wannan zai taimaka ga mai son rage kiba cika burin sa.

A Wasu Kasashe, Saboda Tsananin Yawan anfani da suke yi da Lemun Tsami, yana da matukar wuya a samu mai karancin sinadarin Bitamin a jiki.

Karancin sinadarin na Sanya kamuwa da larurori Kamar Yawan Gajiya, Zubar Jini a Dadashi, Kuraje a Fata, Ciwon Gaba, Kurajen da basa  Warkewa, Murdaddun Gashi, Ciwon Damuwa, Zubewar Hakori, da Karancin Jini a Jiki.

Ruwan lemun tsami shim yana da alfanu ga jikin dan adam sosai. Saboda tsamin sa, yana Sanya yawan sinadarin tsami a cikin fitsari. Wannan na rage Hadarin Kamuwa da Ciwon Duwatsun Koda Wato Kidney Stone.

Anfani da lemun tsami fiye da masala na da illa ga lafiyar jiki. Kiyaye anfani da lemun tsami na da Muhimmanci sosai ga Mai Ciwon Gyanbon Ciki, Kurajen Baki, ko Ciwon Hakori.

Anfani da lemun tsami Dai-Dai kima na Samar da kariya daga cututtuka da dama da kuma inganta lafiyar jikin dan adam. Sannan bin shawarwari ga masu shan wasu magungunan asibiti na da muhimmanci.

 

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos