Home ยป Lafiyar Qashi

Inganta Lafiyar Kashi ta hanyar cin abinci masu dauke da sinadarai masu anfani ga kashin. Lafiyar kashi na nufin lafiyar jiki. Kashi shine ginshin dake rike da dukkan jikin dan adam.

Ga Mata, lafiyayyen kashi na da matukar muhimmanci, musamman a lokacin da shekaru suka soma ja. A wannan lokacin ne kashin ke tsananin bukatar kulawa saboda kiyaye kai daga cututtuka da dama kamar su Rashin Kwarin Kashi.

Sinadarin Kalshiyom (Calcium) na daga cikin manyan sinadarai da kashi ke bukata. Kaso mafi girma na kashi sinadarin Kalshiyom ne. Anfani da abubuwa masu kunshe da wannan sinadarin zai taimaka wajen kara karfin kashi. Sannan kuma zai taimaka wajen rage hadarin Saurin karaya da kuma cutar rashin kwarin kashi.

Madara na cikin abubuwa dake inganta lafiyar kashi. Anfani da Madara, Yogot da Cukui na wadata jiki da sinadarin kalshiyom. Ga wadanda basa anfani da madara, Almon, Brokoli da wasu Ganyayyaki zai wadata jikin su da sinadarin kalshiyom da ake bukata.

Sinadarin Bitamin D na taimakawa wajen tatsar sinadarin Kalshiyom daga cikin abinci. Ana samun sinadarin Bitamin D cikin zama a hantsi. Sannan kuma cin Kifi mai Maiko, Kwanduwar Kwai, Lemu da wasu nau`ukan Hatsi na wadata jiki da sinadarin Bitamin D.

Sinadarin Frotin dake cikin abincin da muke anfani da shi na taimakawa wajen gina kashin da kuma warkar da rauni a kashi. Anfani da Nama, Kaza, Zaabo, Kifi, Kwai, Dangin Gyada, da sauran Abubuwa Dake kunshe da sinadarin Frotin. Sinadarin Bitamin K na taimakawa jiki ya samu damar tatsar sinadarin Frotin cikin abinda aka ci.

Koren Ganye Kamar Alaiyahu, na wadata jiki da sinadarin Bitamin K. Bincike ya nuna cewar Bitamin K na da matukar anfani wajen lafiyar Kwankwaso. Matan da suka manyanta na tsananin bukatar wannan sinadarin a jiki.

Shima Sinadarin Magniziyom na taimakawa lafiyar kashi. Ana samun wannan sinadari a cikin Dangin gyadya, Hatsi, Wake da Koren Ganye.

Cikin abincin da muke ci zamu samu wadatar lafiya mai inganci. Lura da lafiyar kashi abu ne da ke da matukar anfani musamman ga mata da kuma wadanda shekaru ya ja.

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos