Home » Lafiyar Hanta

Hanta Wata Muhimmiyar Sashe ce a Jikin dan adam. Kula da Lafiyar Hanta ya na da muhimmanci sosai.

Abincin da muke ci a rayuwa na da tasiri sosai dangane da lafiyar dukkan sassan jikin mu. Saboda haka, hanta ita ma ba a barta a baya ba.

Saboda Muhimmancin Aikin ta a Jikin dan adam, ya zama dole mu kula da lafiyar ta a koda yaushe.

Akwai nauoin abincin da ya kamata mutum yayi anfani da su domin inganta lafiyar hantar sa. Sannan akwai kuma wanda ya kamata mutum ya guje musu.

Nauin ganyayyaki kamar su Alaiyahu da salat na taimakawa wajen inganta lafiyar hanta. Ganyayyaki kamar su brokoli, kabeji da sauransu su ma na bada sinadaran da ke inganta lafiyar hanta.

Har wa yau Mongoro, Lemo, Kankana, gwanda, gwaiba da inibi na daga cikin abubuwan da ke kare lafiyar hanta. Dangin sturoberi, Dankali, karas, abokado da tumaturi suma baa bar su a baya ba.

Abin mamaki, shayin kowfi wanda ake ganin bashida wani anfani a jiki na taimakawa wajen kare mutum daga kamuwa da cututtukan hanta har ma da dajin hanta wato kansa.

Shan shayin koren ganyan shayi na da muhimmanci wajen inganta lafiyar hantar. Sai dai yana da kyau a kimanta shan sa domin shan sa da yawa kan zama illa.

Hanta na bukatar wasu nauin abinci masu maiko kamar su kifi da dangin gyada.

Babban abin da ke kawo matsala ga lafiyar hantar dan adam shine shan giya barasa. Ita giya wato barasa kan haifar da dajin hanta ga masu shan ta. Shan Suga, gishiri da soyayyan abinci dukkannin su na haifar da matsala ga lafiyar hantar mutum.

Baya Ga Haka, shan lemon kolba masu dauke da karin suga barazana ce ga lafiyar dan adam. Kara gishiri ko zuba shi da yawa a cikin abinci illa ne sosai ga lafiya. Yawan anfani da abincin gwangoni ko wasu naui da aka sarrafa su abu ne da kamata a guje su.

Babban yanayi da zamu kula da hantar mu shine ta hanyar abincin mu. Ingantaccen abinci mai kunshe da yayan itatuwa, ganyayyaki, koren shayi da na Coffee da dangin gyada.

images
Abincin Don Kula Da Lafiyar Hanta 

A Kauracewa shaye-shaya, a Rage yawan shan suga, gishiri, soyayyen abinci da na gwangoni  don kare kanmu daga Kamuwa Da cutar hanta.

Kada mu manta, lafiyar hantar mu tana hannun mu. Mu kiyaye ta, ta hanyar cin ingantaccen abinci.

Yabintu Abubakar

View all posts

Add comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos