Home ┬╗ KUSKURE CIKIN SHAN MAGANI

Kuskure Cikin Shan Magani ko Sha Fiye da Kima. Mutane Kan yi Kuskure Wajen Shan Maganin da ba shi ake Bukata ba. A Wani Lokacin Kuma Wanda ake Bukatar a Sha, Sai A Kuskure a Sha Fiye da Adadin da ya Dace a Sha.

Hakan na Kasancewa Babbar Matsala ga Lafiya da ma Rayuwarmu Baki Daya. Lokacin da za`a sha Magani, Yana da Muhimmanci a Kula da bin Ka`idojin da Likita ya Shimfida Dangane da Maganin.

Wasu Magungunan Kan Haifar da Matsala idan aka Hada su da Wasu Daban Musamman a in aka Hada Su Da Na Gargajiya. A Wani Lokacin Shan Magani Cikin Maye Kan Haifar da Mummunar Matsala ga Mutum.

Kimanin Mutane da Dama na Mutuwa Sakamakon Shan Magani Fiye da Kima.

Bincike Ya Tabbatar Cewa a Duk Lokacin Da Mutum Ya Sha Magani Fiye Da Kima, Ayyukan Da Maganin keyi a Jikinsa Zai Dinga Ninkawa ne. Wanda zai zamo illa ga Asalin Halittar Mutum. Amma akan Iya Samun Mafita Dangane da Wannan Al’amari.

Duk Da Cewa An san Magani Waraka ne, Amman yana Dauke da Sinadaran da kan Iya Cutar wa Lokacin da Sukayi Yawa a Jiki.

Kuskure cikin shan magani na Faruwa ne a Lokacin da aka sha Maganin Cikin Rashin Sani. Ko kuma Shan Wani a Madadin wani Daban da Ba shi ake so a Sha ba, Shan Fiye da Adadin da Likita ya Fada. Hada shi da wani Wanda ba sa Haduwa duka na nufin Kuskure ne. Kuma  Dukkannin su kan Haifar da Matsala ga Wanda ya Sha. Har ila yau, ana iya yin Kuskure Dangane da Yin Aiki Ko Tiyata ga Mutum.

A wani lokacin Shan Magani Daban guda Biyu Masu Anfani iri Daya a Jiki ko Masu Dauke da Sinadarai iri Daya na Kasancewa Sha Fiye da Kima Saboda Aiki iri Daya Zasu Gudanar a Jiki. Wasu Magungunan na da Suna iri Daya Amma Kafin Wani ya Wuce na Wani. Kuskuren Daukar Babba a Matsayin Karami kan Haifar da Matsala ga Wanda ya Sha.

Mutanen da ke da Mantuwa ko Wasi-Wasi kan shan Magani sau biyu ko fiye da haka a lokacin da suka manta da cewar sun sha na wannan lokaci.

A yara kanana, ana samun irin wannan kuskuren lokacin da iyaye suka yi kuskuren bada shekarun yaro ga likita. Likitan zai bada maganinne bisa ga shekarun wanda hakan zai iya zamo illa ga yaron maganin ya fi karfin jiin sa.

Sakacin Ajiye Magani na Iyaye a Wajen da Yaro zai iya dauka na da hadari. Sannan a duba maganin sosai ko da kai ka ajiye kafin a bawa yaron zai taimaka.

Wasu daga cikin alamomin shan magani fiye da kima sun hada da, Sarkewar Numfashi ko Rashin Numfashi, Suma, Minshari ga Wanda bai Saba yi ba, Gushewar Hankali, Canza Launin Lebba ko Yatsun Hannu. Mutuwar Jiki, Hannu ko Kafafuwa, Kafewar Idanu duka Wadannan Suna Daga Cikin alamomi dake nuna an Sha Magani Ba bisa ka’ida ba.

Yawancin iyaye na sakaci da bawa yara maganin ciwon jiki na farasitamol akai-akai. Bincike ya nuna cewar wannnan na daga cikin abubuwan da ke kashe yara kanana cikin sauri. Ya kan sanya fatar jikin su ta canza launi har ma da idanu a lokacin da yayi yawa a jiki.

Yana da muhimmmanci a gaggauta kai wanda ya yi kuskuren shan magani fiye da kima asibiti. Kafin a kai ga asibitin a kwantar da shi ta gefe, a dinga yi musu Magana, a kwance duk wani waje ajikin su da kan takura musu kamar wuyan riga ko maballin riga, a samu wadatar iska a inda suke ko da ta hanyar fifita ne. In ta kama za`a yi musu dannan kirji ga wanda baya nunfashi ma`ana bada agajin gaggawa.

Yana da muhimmanci a ajiye magani a wuri mai kyau da kuma nesa da inda yara zasu dauka. A duba sosai kafin a sha don tabbatar da wanda ake so a sha. Fahimtar hada wannan maganin da wani nada anfani, a auna yadda ya dace ga magungunan yara. A tambayi likita yaushe ya dace a rage shan maganin ko kuma dakatar da shi.

A ko wani lokaci, bin dukkan ka`idojin shan magani na da muhimmanci sosai domin kare rayukan mu.

Yabintu Abubakar

View all posts

1 comment

Leave a Reply

Waraka Radio

Latest videos